Ƙungiyar haɗa Kai da zaman lafiya ta Arewa (ACI) ta roƙi Gwamnatin tarayya da ta kawo karshen kashe-kashe da garkuwa da mutane, da lalata rayuwar al’umma a yankin Arewa, tana mai cewa, ya dace a daina magance matsalar rashin tsaro da fatar baki kawai.
Darakta Janar na ACI, Dakta Abdullahi Idris ya bayyana hakan a taron manema labarai a Kaduna ranar Lahadi, a yayin bikin “Ranar Zaman Lafiya ta Duniya ta shekarar 2025”, yana mai jaddada cewa dole ne a daina murna da bambance-bambancen da ke tsakanin al’umma, a magance ƙorafe-ƙorafe ta hanyar da ta dace, sannan a haɗa al’umma cikin girmamawa da mutunta juna.
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Bayyana Ra’ayin Kasar Kan Rikicin Falasdinu Da Isra’ila
- Yadda Ƴan Agbero’ Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Abuja
“Tsawon ƙarni da dama, ‘yan Arewa suna rayuwa tare cikin zaman lafiya duk da bambancin addini, kabila da al’adu. Ba za mu lamunci yan siyasa masu son rai ko masu cin gajiyar rikici su haddasa gaba tsakanin ‘yan uwa ba.
Ya gargadi cewa, tarihi ba zai gafarta wa shugabannin Arewa ba idan suka kasa daukar matakin gaggawa wajen dakile kashe-kashe, garkuwa da mutane da rikice-rikicen da ke addabar yankin. Ya ce shiru da fifita wasu akan wasu daga cikin shugabanni suna kara ta’azzara matsalar tsaro a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina, Filato da Benuwe.
Ya bayyana cewa akwai damuwa matuka yayin da ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar al’umma, wasu daga cikin manyan mutane na fifita shirya shagulgula masu tsada maimakon kiraye-kirayen tarurrukan neman mafita na gaske don kawo karshen wannan rikici.
“Lokacin yin shiru ya wuce, yanzu ne lokacin daukar mataki. Tarihi ba zai gafarta wa halin ko-in-kula ba a lokacin da ake bukatar mataki fiye da kowane lokaci.”
Idris ya ce kungiyarsu na cikin damuwa matuka bisa abin da ya kira “ƙin ɗaukar mataki na gaggawa daga hukumomin tsaro duk da bayanan sirri da ke hannunsu, lamarin da ya bar gwamnonin jihohi cikin wahala da kuma barin ‘yan kasa cikin hali na shakku da rashin tsaro:.
Ya kuma bukaci ‘yan Arewa da su kaurace wa rarrabuwar kawuna, yana mai jaddada cewa tsawon ƙarnuka mutane masu bambancin addinai da kabilu sun zauna tare cikin zaman lafiya.
Har ila yau, dole ne a fahimci zaman lafiya ba wai kawai rashin rikici ba ne, har da nufin kasancewar adalci, da mutunci ga kowa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp