A ranar Alhamis din da ta gabata ne Majalisar Zartarwar Jam’iyyar Labour ta Jihar Ogun ta kori Darakta-Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa, Dakta Doyin Okupe, da wasu mutane 11 saboda kin biyan hakkokinsu na zama mamba a Jam’iyyarsu ta LP.
A cewar SEC, wacce ta bayyana hakan bayan wani taro a Abeokuta, ta ce matakin ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
- Tinubu Ya Bukaci Manyan Masu Kalubalantarsa Atiku Da Obi Da Su Janye Daga Takara
- Peter Obi Na Goyan Bayan Hako Man Fetur A Yankin Arewa Maso-Gabas
Wadanda aka kora tare da Okupe sun hada da
Abayomi Collins, Hon. Abel Olaleye, Jagun Lookman, Olori Oluwabukola Soyoye, Mr. Gbadebo Fesomade, (tsohon ma’ajin jihar) da Mista Abdulmalik Olaleye (tsohon shugaban matasan jihar).
Sauran sun hada da Mista Jide Amusan (tsohon Sakataren Yada Labarai na Jiha) da Mista Adeshina Wasiu Shojobi (Tsohon Shugaban Matasan Jihar) da kuma Miss Deborah Adewale, (Tsohuwar Shugabar Mata ta Jihar Ogun ta Gabas) da Mista Olatunde Abolade (Tsohuwar Sakatariyar Jiha).
Da yake yi wa manema labarai jawabi a Abeokuta, shugaban jihar; Michael Ashade da Feyisola Michael; Sakataren Jam’iyyar na Jihar, ya yi zargin cewa Okupe da sauran wadanda aka kora sun ki aabanta biyansu hakkokinsu na zama memba a Jam’iyyar, duk da tunatarwa da aka yi ta musu cewa ya kamata su tabbatar da sun sabanta zamansu na mamba a Jam’iyyar ta hanyar biyan kudaden harajin Jam’iyyar.