Kwanan baya, yayin da shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva, ya zanta da wakilin babban gidan rediyo da talebijin na kasar Sin na CMG, ya bayyana cewa, kasar Sin na neman tattaunawa da sauran kasashe domin samun ci gaba, a maimakon ingiza tada yake-yake. Ko shakka babu duniya na bukatar kasar Sin.
Shugaban ya kara da cewa, kasar Sin ta nuna karfinta a kusan dukkanin fannonin tattalin arziki, da kimiyya da fasaha, da samar da kayayyaki da ayyukan injiniya, lamarin da yake da matukar muhimmanci ga kasashen duniya, saboda duniya na kunshe da sassa daban daban a maimakon wani bangare guda.
Shugaban ya ce bai kamata a saurari murya daya, ko a lura da kasa daya kacal ba. Kasar Sin na neman tattaunawa domin samun ci gaba, a maimakon ingiza tada yake-yake. Tana mai da hankali kan zuba jari, da bada ilmi, da horar da injiniyoyi, da masana ilmin halittu, da likitoci, da kwararru a ilimin sararin samaniya, tana kuma takara da wadanda a baya suka kasance kan gaba a duniya.
Hakan yana da muhimmanci sosai, kuma yana amfanar da duniya. (Tasallah Yuan)