Ma’aikatan jihar Ribas sun hallara a sakatariyar kungiyar kwadago ta kasa, NLC da ke Fatakwal domin bikin ranar ma’aikata ta 2025 a ranar Alhamis.
Dama kungiyar ta NLC, tuni ta sanar da cewa, ba za ta gudanar da bikin murnar ranar ma’aikata ba kamar yadda aka saba yi a filin shakatawa na Isaac Boro, inda a al’adance kungiyoyin kwadago daban-daban ke gudanar da tattaki a filin domin murnar wannan rana ta 1 ga watan Mayu.
- Gobara A Haramtacciyar Wurin Ajiye Man Fetur Ta Ci Rayukan Mutane 5 A Jihar Ribas
- Aikin Gina Tashar Jirgin Ƙasa A Kano Yana Ci Gaba Gadan-gadan
A maimakon haka, ma’aikatan sun taru ne domin nuna goyon bayansu ga Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa da ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas a sakatariyar kungiyar NLC ta jihar.
In ba a manta ba, LEADERSHIP ta rahoto cewa, Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa da ‘yan majalisar dokokin jihar, inda ya mika jihar karkashin kulawar tsohon shugaban sojin Ruwa na Nijeriya.
Dukkan kungiyoyin NLC a jihar, sun yi taro a sakatariyar da ke kan titin Igboukwu, D-Line, Fatakwal, inda suka bayyana rashin amincewarsu da abin da suka kira zagon kasa ga mulkin dimokradiyya a jihar Ribas.
A halin da ake ciki, Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Sir Fubara ya yi kira da a ci gaba da kare hakkin ma’aikata a jihar.
Fubara, ya yi wannan kiran ne a cikin sakon hadin kai da jinjinawa da ya bayar a Fatakwal, a daidai lokacin da al’ummar kasar ke bikin ranar ma’aikata ta bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp