Ma’aikatan Jihar Filato sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani bayan gwamnatin jihar ta kasa biya musu bukatunsu.
An ayyana matakin ne a cikin sanarwar yajin aikin da kungiyar hadin gwiwa ta JNC reshen Filato ta fitar a daren ranar Laraba a Jos.
- Gwamnati Za Ta Kashe Biliyan 22.44 Kan Ciyar Da Fursunoni A 2023
- Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Sake Amince Masa Ya Ci Bashin Dala Miliyan 800
Sanarwar da Shugaban JNC na Filato, Titus Malau da Sakatare, Timothy Gopep suka sanya wa hannu, ta ce yajin aikin ya biyo bayan karewar wa’adin kwanaki bakwai da gwamnati ta yi wa’adin kwanaki hudu.
Sun ce an sanar da wa’adin da karin wa’adin ne a cikin wasikunsu na ranar 19 ga watan Afrilu, 2023 da 3 ga watan Mayu, 2023.
Jami’an JNC sun bayyana cewa majalisar ta gudanar da taro a ranar 10 ga watan Mayu tare da shugaban ma’aikatan gwamnati da sakataren gwamnatin jihar.
“A bayyane yake cewa gwamnati ba ta nuna isashen kudurin magance matsalolin ba kamar yadda aka gabatar a cikin kundinmu na bukatu kafin wa’adinta ya kare, kamar yadda ta yi alkawari tun farko.
“Duk da haka, bayan ganawar hadin gwiwa tsakanin JNC da shugabannin kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), an yanke shawarar cewa za a shiga yajin aikin.
“Wannan matakin ya zama wajibi tun da gwamnati ta yi watsi da nata bangaren na yarjejeniyar duk da alkawuran da ta dauka.
“Saboda haka, muna ba da umarnin duk kungiyoyin hadin gwiwarmu da suka fara yajin aikin daga tsakar daren 10 ga Mayu 2023,” in ji su.
A cewarsu, an umurci dukkan kungiyoyin hadin gwiwar da su bi ka’ida tare da tabbatar da cikakken yarda har sai an biya bukatun ma’aikata.
Duo ya yi gargadin cewa duk wani sabawa umarnin zai jawo hukunci mai tsanani.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa ma’aikatan na fafatawa da gwamnatin jihar kan rashin biyan albashi, da dai sauran wasu bukatu da dama.