Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya ta Nijeriya (NANNM) ta janye yajin aikin da ta fara a faɗin ƙasar nan bayan gwamnatin tarayya ta bayyana ƙudirinta na cika muhimman buƙatun da ƙungiyar ta gabatar.
Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wata takarda bayan wani taron kwamitin zartarwa na ƙasa da suka gudanar ta Internet a ranar Asabar.
- Gwamna Fintiri Ya Karrama Kocin Super Falcons, Madugu Da Naira Miliyan 50
- Sauya Sheƙa: Sanatoci Biyu APC Ke Buƙata Wajen Samun Kashi Biyu Cikin Uku A Majalisar Dattawa
Takardar ta bayyana cewa sun yanke shawarar janye yajin aikin ne bayan nazarin abubuwan da aka tattauna a taron da gwamnatin tarayya a ranar Juma’a, 1 ga watan Agusta.
Taron ya samu halartar ministocin lafiya, na ƙwadago da ayyuka, da sauran manyan jami’an gwamnati.
A ƙarshen taron, an rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ta ƙunshi tsare-tsaren cika buƙatun ƙungiyar guda tara tare da jadawalin lokacin cika su.
A cewar NANNM, sun dakatar da yajin aikin ne domin ci gaba da tattaunawa bisa alƙawarin da gwamnati ta ɗauka na aiwatar da buƙatun cikin ƙanƙanin lokaci.
Takardar ta ce, “Kwamitin zartarwa na ƙasa ya yaba da matakan da gwamnatin tarayya ta fara ɗauka, musamman yadda ta bayyana lokacin da za ta aiwatar da buƙatunmu guda tara da muka gabatar.”
Takardar da shugaban ƙungiyar NANNM, Kwamared Haruna Mamman, da sakataren janar, Dr. A. Shettima suka sanya wa hannu, ta umarci mambobinsu da su koma bakin aiki nan take.
Haka kuma shugabannin na ƙasa za su ci gaba da lura da yadda gwamnati za ta cika alƙawuran da ta ɗauka.
Ƙungiyar ta kuma gargaɗi duk wata cibiyar lafiya ko hukuma da ta nemi hukunta ma’aikatan jinya, masu koyon aiki ko na wucin gadi saboda shiga yajin aikin.
Ta ce dukkan mambobinta sun yi amfani da ‘yancinsu na yajin aiki bisa doka.
Ƙungiyar ta yaba da goyon baya da haɗin kai da mambobinta suka nuna a lokacin yajin aikin na kwanaki bakwai, wanda aka fara a ranar 29 ga watan Yuli, 2025.
Yajin aikin ya haifar da tsaiko sosai ga ayyukan jinya a asibitocin gwamnati a faɗin Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp