Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Hukumomin Gwamnati da Kamfanonin Gwamnati (SSASCGOC), reshen Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta ƙaddamar da shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani kan rashin magance batutuwan walwala na ma’aikata.
A cewar wata sanarwa da aka fitar ranar 4 ga Oktoba, 2024, ƙungiyar ta bayyana gazawar shugabancin hukumar wajen warware matsalolin da suka shafi ƙarin girma, da albashi, da walwalar ma’aikata duk da tattaunawa da aka yi a baya.
- An Shawarci NAFDAC Ta Bullo Da Dabarun Fasaha Wajen Yaki Da Jabun Magunguna
- NAFDAC Ta Yi Bikin Lalata Kayayyakin Jabu Na ₦985.3m A Kano
Kungiyar, ta hannun Sakataren TUC, Kwamared (Dr.) Ejor Michael, ta sanar da cewa yajin aikin zai fara ne daga ranar Litinin, 7 ga Oktoba, 2024. Wannan matakin ya biyo bayan cikar wa’adin kwanaki 14 da aka bai wa shugabancin NAFDAC a ranar 20 ga Satumba, 2024. SSASCGOC ta jaddada cewa ba za a bari kowane ma’aikaci ya shiga wani ofishin NAFDAC ba yayin yajin aikin.
Sanarwar ƙungiyar ta yi kira ga dukkan ma’aikatan da su bi umarnin yajin aikin, tare da cewa za a ci gaba da yajin aikin har sai an cika dukkan buƙatun da aka gabatar a cikin sanarwar da aka fitar a baya.
Haka zalika, an umarci dukkan shugabannin jihohi da na yankuna da su tabbatar da cikakken bin wannan umarni na yajin aiki.