Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ta sanar da cewa, ba wai kawai ta mayar da hankali kan kayan aikinta da kuma yin amfani da fasar zamani bane, har da inganta rayuwar ma’aikatan NPA, duba da cewa, sune kashin bayan samar wa da Hukumar ci gaba.
Ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata, a yayin wani taron bikin sanya ido wato NMA da ya gudana a ranar Litinin a shalkwatar Hukumar da ke a jihar Legas.
- Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i
- Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu
Dantsoho wanda Babban Darakta a sashen kudi da gudanar da harkar mulki Dakta Bibian Richard-Edet, ya wakilce a wajen taron ya sanar da cewa, taron ya tabbatar da gagaruwar ci gaban da Hukumar ta samu, wajen gina rayuwar ma’aikatan NPA da kuma daga darajar samar da ilimin zamani domin kara daga kwarewar ma’aikatan.
A cewarsa, yayin da Hukumar ta NPA, ke ci gaba da zuba hannun jari wajen samar da ingantattun kayan aiki da suka mataki irin na duniya, ta hanyar yin amfani da fasahar zamani, dole kuma ta mayar da hankali, wajen kula da inganta rayuwar ma’aikatanta.
“Kasancewar Hukumar ta NPA tamkar kafar ci gaba da bunkasa tattalin arzikin kasar nan, na cikin Teku, mun kuma mayar da hankali wajen samar da kayan aikin na fasahar zamani, tare da kuma kara ingnata kula da rayuwar ma’aikatan mu, “ Inji Dantsoho.
Shugaban ya kuma yaba bisa gudunmawar da kwararrun matasa ke samar wa, musamman masu yiwa kasa hidima da ke yin aikin yiwa kasa hidama, a Hukumar ta NPA.
Ya danganta su a matsayin matasan gobe da za su samar da sauyi wajen ci gaba da bunkasa fannin tattalin azrki na Teku da kuma ga daukacin tattalin arzikin kasar nan.
An kirkiro da wannan ranar ta NMD ce, a shekarar 2014 wadda kuma aka kaddamar da ita a kasar Ingila a shekarar 2016, wadda kuma ake gudnar da bikin zagoywar ranar, a duk ranar 27 na watan Okutobar kowacce shekara.
Kazalika, gudanar da bkin wannan ranar, ta yi daidai da cimma muradun karni, na Majalisar Dinkin Duniya.












