Ma’aikatan Sufurin Jiregen Sama ya yi tir da dabtarin kudin yarjejeniyar sayar da hannun sayar da hannun jarin daukacin Tashoshin Jiragen Sama na kasar.
Sun sanar da cewa, akwai rashin bin ka’ida da masu ruwa da tsaki a fannin suka yi kan wannan batun.
- Ba Sulhu Ko Sassauci Ga Ƴan Bindiga A Zamfara – Gwamna Lawal Dare
- Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Kaduna Ta Yi Watsi Da Kalaman El-rufa’i Akan Zargin Maguɗin Zaɓe
Ma’aiktan sun bayyana, yarjejeniyar ta sabawa ka’ida kuma ‘ya’yan kungiyar, ba su da wata masaniya kan batun.
Kazalika, sun soki Gwamnatin Tarayya kan zagaye Ma’aikatan da kuma sauran kungiyoyin na da ke tafiyar da Sufurin Jiragen Sama tare da kuma yin watsi da bukatun Ma’aikatan.
A cewar, Ma’aiktan bisa ka’ida kamata ya yi Gwamnatin Tarayya ta wallafa batun na yarjejeniyar a manyan Jaridun kasar kasar a matsayin talla har zuwa tsawon watanni shida yadda duk wani mai bukata shiga cikin yarjejeniyar zai samu damar shiga cikin sahun masu nema
A farkon wannan shekarar da ta gabata, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito Ministan Sufurin Ma’aikatar Jiragen Sama Festus Keyamo, a wani taro ya bai wa kungiyoyin na Sufurin Jiragen Sama tabbacin cewa, Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da bi ka’ida wajen sayar da hannun jarin Tashoshin Jiragen Saman kasa.
Keyamo ya kuma bai wa shugabannin kungiyoyin tabacin cewa, suma a sanya kan batun na yarjejeniyar ta sayar da hannun jarin Tashoshin Jiragen Saman.
Kazalika, ba su tabbacin cewa, zai umarci hadiminsa domin ya ci gaba da sanar da shugabannin kungiyoyin kan abinda ke tafiya game da yarjejeniyar.
Sai dai, a jawabin da shuwagabbin kungiyar da kuma na ma’aikatan suka gabatar a wani babban taronsu a shalakwar Tashar Jiragen Sama da ke a jihar Legas, sun soki Ministan Sufurin Ma’aikatar Jiragen Sama Festus Keyamo, bisa zagaye shugabannin kungiyoyin kan batun na jarjejeniyar.
A jawabinsa shugaban kungiyar ma’aikatan zirga-zirga ta jiragen sama na kasa NUATE Kwamarade Ben Nnabue ya yi kira da sake sabon lale kan batun na yarjeniyar musamman domin a bai wa sauran masu ra’ayin shiga cikin yarjejeniyar.
“Ya kamata a sake faro yarjejeniyar tun daga farkonta, domin a bai wa sauran ‘yan Nijeriya damar shiga cikin yarjejeniyar,”Inji Shugaban.
Nnabue ya ci gaba da cewa, a matsayinsu na shuwagabannin kungiyoyin sam ba su da wata masaniya game da wannan yarjejiniyar da da Gwamnatin ta kulla.
Ya kara da cewa, hatta shuwagabannin kungiyoyin kwadago ba a sanar da su, game da yarjejiniyar ba, amma sai kawai muka ji, Ministan Sufurin Ma’aikatar Jiragen Sama Festus Keyamo, sanar da cewa, Majalisar Zartwar kasar ta amince da wannan yarjejeniyar, musamman ta Tashar Jirgin Sama na jihar Enugu.
“Muna son mu sanar da duniya cewa, dole kafin a gudanar da duk wata yarjejniya a fara tattaunawa da shuwagabbin kungiyoyin kwadago tukunna, ” A cewar Kwamarade Ben.
Ya sanar da cewa, hanyoyin da ake bi na gudanar da wannan yarjejeniyar, cike take da kura-kurai domin ba mu da wata masaniya ko an bayar da talla ga manyan Jaridun kasar nan kan batun na yarjeniyar.
“Tashoshin Jiragen Sama na kasar nan, mallakin ‘yan Nijeriya, a saboda haka ba za ta sabu kawai a cikin dare daya mu ji an yanke shawarar cewa, akwai wasu ‘yan lele da ake so su kadai a yi yarjejeniyar da sub a, domin kamata ya yi ba bar abin a bude domin suma ‘yan kasar, su gyada ta su sa’ar, a saboda haka, muna bukatar a soke wannan yarjejniyar har sai idan an bi ka’idar da ta dace, “ Inji shugaban.
Shi ma a na sa bangaren shugaban kungiyar kwarru ta ANAP Kwamarade Alale Adedayo, ya yi tir da hanyoyin da Ministan ya bi domin yin wannan yarjejeniyar ba tare da janyo shugabannin kungoyoyin ba kamar yadda ya yi masu alkwari a baya.
Kwamarade Adedayo ya bukaci da sake sabon lale kan batun wannan yarjejeniyar, musamman domin a tabbatar da an bi ka’aida da kuma yin gaskiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp