Ma’aikatan wutar lantarki a Jihar Katsina sun fara yajin aiki saboda rashin biyan su kuɗaɗen fansho na sama da shekaru takwas.
Yajin aikin wanda Ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ke jagoranta, ya fara ne a ranar Laraba, kuma ya shafi ma’aikatan kamfanin rarraba wuta na Kano (KEDCO) wanda ke samar da lantarki a jihohin Kano, Katsina da Jigawa.
- ‘Yansanda Sun Tarwatsa Wuraren Haɗa Jabun Taki A Bauchi, An Cafke Mutum 5
- Kotu Ta Soke Umarnin Kwace Filin Asibitin Tiamin, Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Diyyar ₦2.6bn
Shugaban yankin Arewa maso Yamma na ƙungiyar, Kwamared Sani Muhammad Ahmad, ya bayyana wa wata jarida cewa sun rufe ofishin KEDCO da ke kan titin Kano a Katsina a matsayin matakin nuna fushinsu, bayan gagarumar ƙoƙari da suka yi wajen tattaunawa da kamfanin amma abin ya ci tura.
Ya ce fiye da watanni 100 ana cire musu kuɗin fansho daga albashin amma ba a biya su ba, kuma kamfanin KEDCO na da isasshen kuɗi da zai iya biyan kuɗaɗen amma yana ƙin yin hakan.
Kwamared Sani ya ce yajin aikin ba zai tsaya ba sai an biya duk kuɗaɗen da ake bin su.
Ya kuma ce suna sane da cewa yajin aikin zai iya shafar jama’a musamman a Katsina.
“Ba ma’aikata kaɗai muke ba – iyaye ne mu kuma masu ciyar da iyali. Abin da muke nema kawai haƙƙinmu ne,” in ji shi.
Yajin aikin zai iya haifar da tsaiko wajen samun wutar lantarki a yankin, musamman a Katsina inda yajin aikin ke da zafi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp