Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ya amsa tambayoyin ‘yan jaridu, dangane da soke takunkumin tattalin arziki da cinikayya da kasar Amurka ta kakabawa kasar Sin.
Kakakin ya ce, bayan tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da aka yi tsakanin kasar Sin da kasar Amurka a birnin London na kasar Burtaniya, cikin ’yan kwanakin nan, bangarorin biyu sun aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a ranar 5 ga watan Yuni, tare da inganta ayyukan da abin ya shafa bisa sakamakon da suka cimma a taron tattaunawar tattalin arziki da cinikayya na Geneva. A halin yanzu, tawagogin Sin da Amurka suna gaggauta aiwatar da sakamakon da aka cimma bisa “tsarin London”. Kana, kasar Sin tana tantance kayayyakin da za ta ba da iznin fitarwa zuwa kasashen ketare bisa dokoki da manufofin da abin ya shafa. Kasar Amurka ma ta dauki matakan soke takunkumin da ta kakabawa kasar Sin, ta kuma sanar wa bangaren Sin bayanai game da hakan.
Da kyar bangarorin biyu suka cimma matsaya daya tare da kulla “tsarin London”, don haka ya kamata a bi hanyar yin shawarwari, maimakon kalubalanta ko tilastawa wani. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp