A baya-bayan nan ne MDD ta fitar da wani rahoto domin tantance yadda ake aiwatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030, inda ta yi nuni da cewa kusan rabin manufofin sun gamu da tafiyar hawainiya wajen samun ci gaba, kuma kashi 18 cikin 100 na manufofin ma sun gamu da koma baya.
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce duniya na fuskantar “halin ni’yasu a bangaren ci gaba”, amma har yanzu za a iya cimma burin da aka sa gaba. Kana mabudin hakan ya ta’allaka ne kan ko dukkan bangarorin da abin ya shafa za su iya daukar matakin gaggawa cikin hadin kai da zai zama tabbatacce.
A yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana a gun taron manema labaru na yau da kullum a yau Alhamis 17 ga wata cewa, matsalar samun ci gaba ta zama kalubale na hakika ga dukkan kasashen duniya. Kuma a koyaushe kasar Sin ta kasance mai fafutukar inganta ci gaban duniya.
Ya ce, “Gwamnatin kasar Sin ta shigar da aiwatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030 a cikin shirinta na shekaru biyar-biyar karo 14, kuma ta cimma manufofin da suka dace a fannin rage fatara, da kiwon lafiya da sauran fannonin da aka tsara tun kafin lokacin da aka tsara kammala su, tare da ba da gudummawa mai kyau wajen aiwatar da harkokin duniya baki daya.”
Ya kara da cewa, “Kasar Sin ta ba da himma sosai wajen inganta hadin gwiwar ci gaban kasa da kasa, da gabatar da shirye-shiryen ci gaban duniya tare da aiwatarwa, da kuma zurfafa hadin gwiwa da cibiyoyin raya kasa fiye da 20 a cikin ’yan shekarun nan, inda sama da mutane miliyan 30 daga kasashe fiye da 60 suka amfana.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp