Yau Laraba, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Game da lambar yabon zaman lafiya ta MDD da rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta Sin dake Kango (Kinshasa) karo na 27 ta samu a kwanan nan, kakakin ma’aikatar wajen Sin, Mao Ning, ta bayyana cewa, Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, kuma za ta ci gaba da shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD take gudanarwa.
- Kasar Sin Ta Jaddada Bukatar Hadin Gwiwa A Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Na MDD
- Matakan Amurka Na Dakile Cinikayyar Ababen Hawa Masu Aiki Da Lantarki Na Sin Za Su Haifar Da Koma Bayan Cinikayya A Duniya
Game da rahoton kwarin gwiwar zuba jari kai tsaye daga kasashen waje na 2024, da wani sannanen kamfanin ba da shawarwari na kasa da kasa mai suna Kearney ya bayar, wanda ya nuna matsayin Sin ya tashi daga na bakwai a bara zuwa na uku a bana, Mao Ning ta bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da kyautata yanayin kasuwancinta, da kuma more ribar kasuwa da ci gabanta tare da sauran kasashen duniya.
Game da kungiyar tarayyar Turai da ta sanar da cewa za ta yi bincike kan kamfanonin kera na’urorin samar da wutar lantarki bisa karfin iska na kasar Sin, Mao Ning ta ce, bangaren Sin na ankare sosai kan manufofi na rashin adalci da bangaren Turai ya sanya don takurawa kamfanoni da masana’antun Sin, bangaren Sin za ta tsaya tsayin daka kan kiyaye moriyar kamfanonin kasar.
Game da dangantakar Sin da Rasha, Mao Ning ta ce, Sin da Rasha suna da ikon gudanar da hadin gwiwar tattalin arziki yadda ya kamata, bai kamata a gurgunta da dakile irin wannan hadin gwiwa ba. (Safiyah Ma)