Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Alhamis cewa, kasarsa ta kara yin kira ga kasar Japan, da ta tinkari damuwar kasashen duniya da ta jama’ar cikin gida, ta dakatar da shirinta na zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku.
Rahotanni sun bayyana cewa, a kwanakin baya ne kamfanin wutar lantarki na Tokyo, na kasar Japan ya tabbatar da cewa, gurbataccen ruwan da aka ajiye a tashar makamashin nukiliya ta Fukushima Daiichi, ya fara yoyo ne saboda wani bututun da ake amfani da shi wajen jigilar ruwan dagwalon nukiliyar ya fashe.
Jami’in ya nuna cewa, kasashen duniya ba su taba dakatar da nuna shakku kan halasci, da tsaro na shirin kasar Japan, na zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku ba.
Gurbataccen ruwa da aka ajiye a tashar makamashin nukiliya ta Fukushima ya sake fitowa fili, lamarin da ke kara ta’azzara damuwar duniya game da gazawar gudanar da ayyukan kamfanin samar da wutar lantarki na Tokyo, da kuma rashin ingantaccen tsari na gwamnatin Japan. (Mai fassara: Bilkisu Xin)