A yau Alhamis, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta sanar da cewa za a soke shirin da aka yi na wayar tarho tsakanin kwamandojin rundunonin sojin kasashen Amurka da Sin da kuma ganawar da za a yi tsakanin ma’aikatunsu na tsaro, tare da sauran wasu matakai.
Haka zalika, kasar Sin ta yanke shawarar kakabawa Pelosi tare da iyalanta takunkuman da suka dace da tanadin dokokin jamhuriyar jama’ar kasar Sin.
Wannan matakin martani ne da Sin ta dauka, saboda nacewar da kakakin majalisar wakilan Amurka ta yi, wajen ziyartar yankin Taiwan, duk da adawa da korafin da kasar Sin ta gabatar. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp