A jiya ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya jagoranci liyafar sabuwar shekara ta 2024 da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta shirya, a cibiyar wasannin fasahohi ta kasa dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin
Sama da mutane 400 ne suka halarci bikin, wadanda suka hada da wakilan ofisoshin jakadanci daga kasashe daban-daban, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Sin, da wakilan sassan gwamnatin kasar.
- CMG Ta Yi Bayani Kan Shirye-Shirye Da Kirkire-Kirkiren Fasaha A Liyafar Bikin Bazara Ta 2024
- Sin Na Ci Gaba Da Taka Rawa A Fannin Makamashi Mai Tsafta A Duniya
Da yake jawabi a yayin liyafar, Wang ya ce, shekarar 2024 na da matukar muhimmanci ga ci gaban zamanantar da kasar Sin daga dukkan fannoni. Yana mai cewa, gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama, buri ne da kasar Sin ke neman cimmawa a harkokin diflomasiyyarta mai sigar kasar Sin a sabon zamani.
Ya ce, a shirye kasar Sin take ta yi aiki tare da dukkan kasashen duniya, wajen tabbatar da tushen zaman lafiya da tsaro, da karfafa zumunci da hadin gwiwa, da bin hanyar da ta dace ta kasancewar bangarori daban-daban, da gina makomar ci gaba da samun wadata.
A nasa jawabin, shugaban jami’an diflomasiyyar kasashen waje dake kasar Sin, kuma jakadan kasar Kamaru a kasar Sin Martin Mpana, ya mika sakon fatan alheri ga jama’ar kasar Sin game da murnar shiga sabuwar shekara a madadin jami’an diplomasiyyar dake kasar. Ya ce, kasashen duniya na fatan hada kai tare, karkashin jagorancin shawarwari guda uku na duniya da kasar Sin ta gabatar, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a duniya baki daya. (Ibrahim).