Yau Jumma’a 18 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi cewa, ba da goyon baya ga ci gaban Afirka wani nauyi ne na bai daya da ya rataya a wuyan kasashen duniya.
Jami’in ya ce, Sin na maraba da dukkan bangarorin kasashen duniya, da su kara mayar da hankali da zuba jari a kasashen Afirka, kana za ta ci gaba da ba da goyon baya ga sanannun kamfanonin kasar Sin masu kwarewa, don fadada zuba jari a Afirka, da taimakawa Afirka wajen kara karfinta, na samun ‘yancin kai da ci gaba mai dorewa, da kuma kama hanyar wadata ta zamani.
Rahotanni sun ce, bisa ga “Rahoton Ci gaban Afirka”, da kungiyar AU, da ta OECD suka fitar tare, an ce, jarin da kasar Sin ke zubawa a Afirka ya kasance kan gaba a duniya. Rahoton ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ita ce kasar da ta fi zuba jari a yankin gabashin Afirka, wadda ke da kashi 20 cikin 100 na jarin waje, sannan ta mamaye matsayi daga na farko zuwa na uku, tare da kasashen Turai da Amurka a sauran yankunan nahiyar, kana muhimman fannonin da take zuba jari sun hada da masana’antun kere-kere, da samar da wutar lantarki, da aikin injiniya, da dai sauransu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)