Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta ba da amsa kan batun fitar da ma’adanan farin karfe na rare earth da sauran batutuwan kasuwanci, inda ta ce matakan takaita fitar da ma’adanan da Sin ta dauka a halin yanzu, abu ne da gwamnati ta aiwatar bisa doka don kyautata tsarin takaita fitar da kayayyaki, kuma ba don wata kasa ko yanki ba.
Kakakin ma’aikatar He Yongqian ce ta bayyana hakan jiya Alhamis, yayin wani taron manema labarai, don mayar da martani kan damuwar wasu kamfanonin Turai da ke jiran amincewar ma’aikatar ta fitar musu ma’adanan farin karfe na rare earth, inda suke fargabar cewa, matakan da Sin ta dauka za su dakatar da ayyukansu.
He Yongqian ta kara da cewa, idan za a yi amfani da ma’adanan don farar hula kuma bisa doka, to Sin za ta amince da bukatunsu. Haka kuma Sin za ta ci gaba da inganta matakan ba da izini da rage tsawon lokacin nazarin bukatu, a kokarin inganta cinikayya masu dacewa.
Dangane da harajin 100% da Amurka ta sanya wa kayayyakin Sin, He Yongqian ta ce, Sin ba ta ji dadin matakan na Amurka ba, kuma tana adawa da su da babbar murya. Ta kuma yi fatan Amurka za ta dauki kyawawan sakamakon tattaunawar ciniki da kasashen biyu suka samu da daraja, ta kuma gyara kura-kuranta nan take. He tana cewa Sin tana son warware matsalolin da ke damun ko wanen bangare ta hanyar tattaunawa bisa tushen mutunta juna.(Amina Xu)