Ma’aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, ma’aikatar za ta ci gaba da ba da cikakkiyar goyon baya wajen gudanar da tsarin taron tattaunawa game da kamfanonin kasashen waje a bana, sakamakon nasarori masu kyau da aka cimma tun lokacin da aka bullo da tsarin a watan Yulin shekarar 2023.
A cewar ma’aikatar, tun bayan da aka kafa tsarin tattaunawar fiye da watanni shida da suka gabata, an inganta sadarwa tsakanin sassan gwamnati, da kamfanonin kasashen waje, da kungiyoyin ‘yan kasuwa na katare, kuma an kaddamar da wasu tsare-tsare masu ruwa da tsaki.
- Wang Yi Ya Yi Tir Da Karairayin Da Ake Yi Game Da Xinjiang A Munich
- Kasar Sin Karfi Ce Ta Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya
Ta ce, ya zuwa karshen watan da ya gabata, ta gudanar da taron tattaunawa 16 da kamfanonin ketare. Kana fiye da kamfanonin waje da kungiyoyin ‘yan kasuwa daga kasashen waje 400 ne suka halarci wadannan tarurrukan, inda aka warware batutuwa sama da 300 a yayin taron.
Ma’aikatar ta ce, a shekarar 2023, darajar jarin waje da kasar Sin ta zuba kai tsaye ta kai dalar Amurka biliyan 163.25, wanda ya kasance a matsayi mai girma a tarihi.(Ibrahim)