Hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Jigawa ta amince da nadin sabbin alkalan kotunan shari’ar musulunci guda 19.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na hukumar, Alhaji Abbas Wangara ya fitar a Dutse ranar Asabar.
- MOFA: Kasar Sin Na Son Sanya Sabon Kuzari A Ci Gaban Tattalin Arzikin Yankin Asiya Da Tekun Fasifik Da Ma Duniya
- Wasu Muhimman Abubuwa Da Ba A Sani Ba Game Da Kwakwalwa
Wangara ya ruwaito sakataren hukumar, Alhaji Auwal Dan’azumi yana cewa, hukumar ta kuma karawa ma’aikata 157 girma.
Sanarwar ta kuma bayyana nadin Nazir Habu a matsayin mukaddashin daraktan kudi na babbar kotun shari’a bayan ritayar tsohon daraktan wanda ya kai shekaru 35 yana aiki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp