Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce ba Sin ce ta haifar da koma bayan alaka tsakanin ta da Amurka ba. Wang ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai na rana rana a yau Talata.
Kalaman na sa na zuwa ne, bayan bullar wasu rahotanni dake cewa, bayan aukuwar takaddamar nan ta balan-balan din Sin da Amurka ta harbo, kasar Sin ta katse tattanawa a matakin diflomasiyya da tsagin Amurka.
A cewar Wang, kamata ya yi Amurka ta dakatar da tsoma baki cikin harkokin gidan Sin, da illata moriyar Sin, kana ta dakatar da nuna tana kare alakar ta da Sin, a hannu guda kuma tana gurgunta tushen siyasa tsakanin kasashen 2. Kaza lika Sin na fatan Amurka za ta yi aiki tare da Sin, domin farfado da kyakkayawar dangantaka da daidaito a alakar sassan 2. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp