Shugaban Faransa Emmanuel Macron na ci gaba da shan matsin lamba daga jam’iyyun adawa har da wasu tsaffin na hannun damansa a kan neman ko dai ya yi murabus ko kuma ya shirya zaben gaggawa na shugabancin kasar. Wannan lamari ya biyo bayan gazawar da Firaministoci har guda bbiyar suka yi wajen kafa tsayayyiyar gwamnati a Faransar.
Tuni dai jam’iyyar Emmanuel Macron ta Renaissance (Re-ne-sans) a shafinta na D ta yi fatali da kiraye-kirayen neman shugaban ya yi murabus don warware rikita-rikitar da siyasar Faransa ke ciki, matsayar da ce babu hankali ciki.
A dazu ne dai jam’iyyar masu zafin kishin kasa ta National Rally RN ta ce babu daya daga cikin jagororinta wato Marine Le Pen ko Jordan Bardella da zai halarci taron da Firaminista Sebestian Lecournu mai murabus ya kira, domin warware rikicin siyasar na Faransa.
‘Yan sa’o’i kafin sanarwar da Jam’iyyar ta RN ta yi ne dai, tsohon Firaministansa Edouard Philippe ya ce yana goyon bayan shirya sabon zaben shugaban kasa a gaggauce.
Wannan matsin lamba dai kari ne kan wadda shugaban na Faransa ke fusakanta daga bangaren masu sassaucin ra’ayi, wadanda su kuma bukatarsu ita ce a zabi sabon Firaminista daga cikinsu.
Sai dai a iya cewa akwai ragowar fatan kawo karshen rudanin da siyasar Faransar ta shiga, la’akari da bayanan da suka ce a dazu an shiga tattaunawa tsakanin jagoran jam’iyyar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya Bruno Retailleau da Firaminista Lecournu, kwana guda bayan murabus din da ya yi. Yayin da kuma a gefe guda rahotanni suka ce a gobe Laraba wakilan masu sassaucin ra’ayi na jam’iyyar Socialist za su gana da Firaminista Lecournun mai murabus.