Madabba’ar PEP ta kasar Sin, ta bayar da gudunmuwar adadi mai yawa na littattafai ga cibiyoyi 13 na koyar da harshen Sinanci dake makarantun sakandare a Abuja, babban birnin Nijeriya, a wani yunkuri na karfafa dangantakar ilimi da al’adu tsakanin kasashen biyu.
Gudunmuwar wadda aka bayar a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin dake Abuja a ranar Alhamis, ta kunshi jerin littattafai sama da 900, na koyon Sinanci da na al’adun kasar Sin cikin harshen Ingilishi, wadanda suka dace da bukatun cibiyoyin. Jami’an da suka halarci bikin mika gudunmuwar sun bayyana ta a matsayin wata gagarumar hanya ta bunkasa shirin koyar da harshen Sinanci a Nijeriya.
Daraktan hukumar kula da ilimin sakandare a birnin tarayya Abuja Muhammed Sani Ladan, ya yaba da gudunmuwar, yana mai nanata kyakkyawan tasirin da za ta dade tana yi kan dalibai da malamai a kasar.
Ya ce ilimi kamar rai yake, kuma ariziki ne da ‘yanci. Ya ce bayar da littattafan tamkar bayar da gudunmuwar rai ne, kuma ya dace da burin kasar Sin na gina kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama.
Dalibai daga makarantun da suka ci gajiyar gudunmuwar, sun gabatar da mabanbantan wasannin al’adun gargajiya na Sin da Nijeriya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp