Tsakanin ranaku 19 zuwa 20 ga watan nan da muke ciki, an gudanar da taron ayyukan raya karkara na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin a birnin Beijing, fadar mulkin kasar. Shugaban kasar Xi Jinping ya halarci taron, inda ya ba da muhimmin umurni kan ayyukan dake shafar raya aikin gona, da karkara, da kuma manoma. Ya ce, ya kamata mu kafa madaidaitan ra’ayoyin aikin gona da na abinci.
Madaidaicin ra’ayin raya aikin gona shi ne raya aikin gona bisa fasahohin zamani, ya dace mu gudanar da harkokin gona ta hanyar amfani da fasahohin zamani da kayan aikin da aka samar bisa bunkasuwar masana’antu na zamani, hakan zai bude wani sabon babi ga aikin gona.
Kana, madaidaicin ra’ayin abinci shi ne habaka ayyukan samar da abinci a dukkan fannoni da kuma ta hanyoyi daban daban, kuma tushensa shi ne hatsi. Kasancewar kasar Sin kasa mai yawan al’umma a fadin duniya, kullum jam’iyya mai mulkin kasar tana mai da matukar hankali kan ayyukan samar da hatsi da manyan amfanin gona, kamar karfafa aikin samar da waken soya da man girki, da kara samar da naman rago da naman sa da madara, da kuma inganta aikin kiwon kifi da sauransu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)