A cikin dogon tarihin bil’adama, binciken sararin samaniya bai taba tsayawa ba, kuma matasa su ne babban karfin binciken sararin samaniya da kuma makomar sana’ar sararin samaniyar bil’adama. Matasan suna cike da nau’o’in tunani game da sararin samaniya, kuma marfarkinsu shi ne bincike da kuma kai ziyara sararin samaniya. A kasashen nahiyar Afirka, akwai irin wadannan matasa da dama, wadanda suka zana mafarkinsu na sararin samaniya, kuma ‘yan saman jannatin kasar Sin sun taimaka musu wajen cimma burinsu.
A watan Maris na shekarar bana, sakatariyar kwamitin aiwatar da matakan dake biyo bayan dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da ofishin kula da harkokin zirga-zirgar kumbunan dake dauke da ’yan saman jannatin kasar Sin a sararin samaniya, da kuma ofisoshin jakadancin kasar Sin dake kasashen Afirka daban-daban, sun gudanar da wata gasar yin zane-zane mai taken “Mafarkin matasan kasashen Afirka”, wadda ta samu halartar matasa fiye da 2000 daga kasashen Afirka guda 42. Daga karshe dai, an zabi zane-zane guda 50 wadanda suka yi fice a gasar.
- ‘Yan Wasan Kasar Sin Sun Lashe Lambar Zinare Ta Farko A Gasar Wasannin Asiya Karo Na 19
- Sin Ta Damu Matuka Da Girgizar Kasar Da Ta Afku A Morocco Kuma Za Ta Taimaka Gwargwadon Karfinta
A ranar 30 ga watan Mayun bana ne, kasar Sin ta yi nasarar harba kumbon Shenzhou-16 dauke da ’yan saman jannati guda uku, inda suka shiga tashar binciken sararin samaniya ta kasar da ake kira “Tiangong”. ’Yan saman jannatin sun tafi da zane-zane guda 10 da matasan Afirka suka yi zuwa tashar, don gudanar da wani aiki mai ma’ana ta musamman, wato baje kolin zane-zanen kasa da kasa a tashar binciken sararin samaniya ta Sin karo na farko. Kuma a halin yanzu, wadannan zane-zane 10 dake bayyana mafarkin matasan kasashen Afirka suna cikin tashar binciken sararin samaniya ta Sin dake da nisa fiye da kilomita 400 daga doron kasa, inda “mafarkin Afirka” ke cikin sararin samaniya a karo na farko.
A ranar 13 ga watan Satumba, sashen kula da harkokin Afirka na ma’aikatar harkokin wajen Sin ya gudanar da bikin bayar da lambobin yabo ga wadanda suka lashe gasar yin zane-zane mai taken “Mafarkin matasan Afirka zuwa sararin samaniya” a Beijing, inda shugaban sashen Afirka na ma’aikatar harkokin wajen Sin, Wu Peng, da mataimakin shugaban ofishin kula da harkokin zirga-zirgar kumbunan dake dauke da ’yan saman jannatin kasar Sin a sararin samaniya, Lin Xiqiang, da jami’an diflomasiyyar kasashen Afirka dake Sin, da wakilan daliban Sin da kasashen Afirka, tare kuma da wasu matasan Afirka da suka lashe gasar, suka halarci bikin.
A yayin bikin, an nuna hotunan zane-zanen da suka yi nasara a gasar. Dukkan zane-zanen suna da kyau kwarai, wadanda suka bayyana ire-iren tunanin matasan kasashen Afirka game da sararin samaniya. Mahalarta bikin da yawa kuma sun dauki hotuna ta wayar salula tare da wadannan zane-zane. Haka kuma a yayin bikin, an gabatar da wani shirin bidiyo game da baje kolin zane-zanen da aka gudanar a tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin wato Tiangong, inda ’yan saman jannatin kasar Sin guda uku suka gabatar wa masu kallo wadannan zane-zanen da matasan Afirka suka zana.
A cikin bidiyon, daya daga cikin ’yan saman jannatin kasar Sin ukun, Zhu Yangzhu dake gudanar da aikinsa a cikin tashar Tiangong, ya yi karin haske kan wadannan zane-zanen, inda a cewarsa, zane-zanen suna nuna sha’awar matasa na kasashen Afirka a kan sana’ar zirga-zirgar ’yan saman jannati a sararin samaniya, al’amarin da ya kara karfafa masa gwiwa ga inganta hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin nazarin harkokin sararin samaniya a nan gaba. Kamar yadda ya ce, binciken sararin samaniya, da bunkasa fasahohin sararin samaniya, sana’o’i ne dake bukatar hadin kan daukacin bil’adama a fadin duniya, ciki har da kasashen Afirka. Yang yana kuma fatan ’yan saman jannati na Sin da kasashen waje za su kara ba da babbar gudummawa wajen gudanar da ayyukan binciken sararin samaniya.
A cikin zane-zanen da aka baje kolinsu a cikin tashar Tiangong, akwai wani zane mai suna “Fata na kowa”, wanda ya samu lambar yabo ta farko a gasar. Wani matashin tarayyar Najeriya ne mai suna Peter Prosper Oshoname ya zana shi, wanda shi ma ya zo Beijing don halartar bikin. A cikin jawabin da Peter ya gabatar a yayin bikin, ya bayyana cewa, “Ina tsaye a gabanku a yau da zuciya mai cike da godiya da farin ciki. Babban abin alfahari ne yadda nake tsaye a nan ina ganin wannan muhimmin lokaci bayan doguwar tafiya daga Najeriya zuwa kasar Sin. Ina mika godiya ta hakika ga wadanda suka shirya wannan gasar zane-zane inda suka samar da wani dandali na bayyana murnar burin yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannin sararin samaniya.”
Ban da nuna godiyarsa, Peter ya kuma ce, wannan gasa ta ba da wata dama ga matasa na kasashen Afirka wajen nuna fasahohinsu na zane-zane, da ba shi kwarin gwiwa wajen cimma burinsa, da samar da babbar dama ta karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin binciken sararin samaniya. Ya kara da cewa, “Wannan gasa ba ma kawai ta baiwa matasan kasashen Afirka damar nuna fasahohinsu a fannin zane-zane ba, har ma ta ba da damar bayyana ra’ayoyinsu game da makomarsu. Muna fatan a nan gaba kuma, Sin da Afirka za su yi hadin gwiwa a fannin binciken sararin samaniya. Mafarkin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin nazarin sararin samaniya, ya haifar da kyakkyawar fata. Lamarin da ke tabbatar da damammakin marasa iyaka a yayin da kasashen suka hada kai tare don cimma buri guda.”
A nasa jawabin, shugaban sashen Afirka na ma’aikatar harkokin wajen Sin Wu Peng, ya yaba da wannan aiki sosai, ganin yadda ya inganta hadin gwiwa mai kyau tsakanin Sin da kasashen Afirka, inda ya ce, “Wannan shi ne karo na farko da tashar binciken sararin samaniya ta Sin ta gudanar da bikin baje kolin zane-zane na kasa da kasa, kuma gasar zane-zane mai jigon ‘Mafarkin matasan Afirka na zuwa sararin samaniya’, muhimmiyar nasara ce da aka samu a yayin gudanar da hadin gwiwa mai kyau tsakanin Sin da kasashen Afirka a sabon zamani. Kana, misali ne na daban, wanda ya shaida sakamakon ci gaba da damammaki da Sin ta raba wa kasashen Afirka a cikin dogon lokaci. Tarihi iri daya da Sin da kasashen Afirka suka taba fama da shi, ya sanya Sin da kasashen Afirka zama tamkar ’yan uwa. Al’ummomin Sin da Afirka suna da buri iri daya, kuma dukkansu suna fatan samun ci gaba da wadata a cikin kasashensu, kana, sun dade da neman zaman lafiya, da bunkasuwa, da hadin gwiwa da samun nasara, shi ya sa Sin da kasashen Afirka suka kasance tamkar abokai dake neman cimma burinsu tare.”
Ban da wannan, jami’in ya bayyana kyakkyawan fatansa ga matasa, inda ya ce, matasa su ne manyan gobe, ba ma kawai akwai bukatar kara karfin horar da matasan Sin da kasashen Afirka ba, har ma akwai bukatar samar da sharudda masu kyau don inganta yanayin ci gaba na matasan. Ya bayyana cewa, “Matasa su ne fata da kuma makomar Sin da kasashen Afirka, kuma su ne ginshikin gudanar da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Burin neman rayuwa mai kyau da ci gaban dangantakar Sin da kasashen Afirka da matasa suke da su, ya kara kuzari ga ci gaban dangantakar abokantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka. Bangaren Sin yana fatan aiwatar da shirin hadin gwiwa na horar da kwararru na Sin da kasashen Afirka da shugaban Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin taron tattaunawa na shugabannin Sin da kasashen Afirka da aka gudanar ba da dadewa ba, don nuna wa kasashen Afirka goyon baya wajen horar da kwararru a kan fanonni iri iri don zamanantar da aikin mulki da bunkasa zamantakewar tattalin arziki da sabunta kimiyya da fasaha da kuma kyautata rayuwar al’umma, da samar da sharudda da yanayi mai kyau ga matasan Afirka don taimaka musu wajen cimma burinsu.”
Game da hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a nan gaba, jami’in ya kara da cewa, a halin yanzu, duniya tana cike da hargitsi, sauye-sauye a cikin karnin da ya gabata suna kara ta’azzara, kuma ba za a iya dakatar da hadin gwiwar kasashe masu tasowa ba. Sin tana sa kaimi ga bunkasuwar sake farfadowar al’ummunta tare da zamanantarwa irin ta Sin, kuma kasashen Afirka suna tafiya cikin sauri zuwa ga buri da ajandar shekarar 2063 da tarayyar AU ta bayyana. Bangaren Sin yana fatan ci gaba da hadin gwiwa tare da kasashen Afirka kan hanyar zamani, da kuma karfafa mu’amalar dabarun samun ci gaba tsakanin juna bisa hadin gwiwar gina shawarar “Ziri da ya da hanya daya” da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da dai sauransu, ta yadda za a samar da manyan damammakin ci gaba ga kasashen Afirka ta sabon ci gaban zamanantarwa irin ta Sin, da samar da yanayi mai kyau don samun ci gaba ga juna.
Idan muka kalli sararin samaniya, za mu ga cewa yana cike da manyan mafarkai. Idan muka kalli al’ummun Sin da kasashen Afirka biliyan 2.6, za a ga yadda hadin kai mai kyau tsakaninsu yake habakawa tare da kawo musu alheri. “Mafarkin matasan Afirka na zuwa sararin samaniya” shi ne mafari, hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka a fannin nazarin sararin samaniyar zai ci gaba da samun kyakkyawan sakamako. Idan matasa suna da akida da karfin hali, hakika kasa za ta samu ci gaba, al’ummar kasar kuma za su samu fata, kuma zumuncin dake tsakanin Sin da kasashen Afirka zai samu kyakkyawar makoma.