- Na Dukufa Samar Da Taskataccen Tarihin Mahaifina
- Burina Na Zama Fitacciyar Mai Shirya Fina-finai
ZAINAB JUMAI ADO-BAYERO, diya ce kuma auta a wajen tsohon Sarkin Kano, Marigayi Alhaji Ado Bayero. Kasancewar ta marubuciya, ta fito da kyawawan tarihin mahaifinta ta hanyar hada wani takaitaccen fim don taskace tarihinsa (documentary) da kuma yadda ya aiwatar da mulkin sarautarsa na tsawon sama da shekaru 50. A wata tattaunawa da ta yi da Jaridar ‘The Sun’ a kwanakin baya, wanda wakilinmu KHALID IDRIS DOYA ya fassara, ta bayyana takaicinta na yadda ake maida mata a matsayin koma baya musamman a harkar shirya fina-finai. Haka nan, ta bayyana babban burinta na zama Babbar Darakta kuma mai shirya fina-finai, sannan ta yi fashin baki kan yadda al’adun Arewa ke tauye wa ‘yan mata burinsu da ra’ayinsu, inda ta nuna adawarta kan takura wa mata da ake yi kan sanya hijabi. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance tare da ita:
Kasancewar ba ki da shekaru da yawa, shin kin san salon mulkin mahaifinki, sannan me za ki iya bayyanawa dangane da sarautar da ya yi tare da dumbin al’adun Masarautar Kano?
Mahaifina marigayi, mutum ne mai mutunci sannan kuma sarkin da ya yi matukar tasiri. Shakka babu, na ga hakan na kuma shaidi hakan tun lokacin da nake tasowa, saboda ya yi sarauta na tsawon shekaru hamsin. Yanzu da na zama cikakkiyar mace, na shiga na fita, na zurfafa bincike tare da yin nazari da dan kankanin ilimina dangane da rayuwarsa. A zahiri ma, lokacin da ya hau kan karagar mulki ba a ma kusan haifata ba; amma na samu damar sanin abubuwa sosai dangane da shi.
A gefe guda kuma, akwai wasu tarin abubuwan da har yanzu ban san su ba dangane da shi. Wannan ne ya sa lokacin da na tsunduma wajen hada tarihinsa (documentary), na fara zuwa na bibiyi rayuwarsa, na kuma zurfafa bincike kwarai da gaske kamar ba mahaifina ba dangane da yadda ya gudanar da rayuwarsa mai ban sha’awa. Binciken nawa ya hada da littattafai da sauran wuraren adana bayanai na tarihi, inda hakan ya ba ni damar gano manyan muhimman abubuwa dangane da shi, wanda hakan ya taimaka min matuka da gaske har ga shi yanzu na samu damar ba da labari a kansa.
Akwai wasu abubuwan da za ki iya cewa kin kwaikwaya a wajen sa ko kina kamanceceniya da shi kasancewar ki na diyarsa?
Babu shakka, akwai abubuwa guda biyu da zan iya cewa na kwaikwaiya ko muna yin kamanceceniya da mahaifin nawa, domin kuwa ina sha’awar karance-karance kamar yadda marigayin shi ma yake son karance-karance. Haka nan, mun yi musharaka wajen son shan nau’in abin sha na soda kamar 7-Up. Sannan na kasance mutum mai kafa-kafa, wadda ba ta kusantar jama’a cikin hanzari kamar yadda shi ma yake.
Kina so ki ce a matsayinsa na wanda ya shafe shekaru sama da 50 kan kan karagar mulki, ba ya kusantar mutane cikin hanzari?
Sosai kuwa, amma yana kusantar mutane tare da janyo su a jiki ne kawai a matsayin sa na sarki. Amma idan ba don haka ba, ko shakka babu zai kasance mutum mai gudanar da rayuwarsa cikin sauki tare da shagaltuwa da abubuwan da ya sanya a gabansa da ya hada da karance-karance da kuma zurfafa tunani kan harkokinsa na yau da kullum. Don haka, a nan bangaren muna kamanceceniya da mahaifina kwarai da gaske.
Mene ne ya baki sha’awa na tunanin taskace tarihin mahaifinki domin tunawa da shi?
Tunda na taso nake matukar sha’awar yawan kallace-kallace da karance-karancen littattafai daban daban. Kazalika, a lokacin da nake makarantar sakandire babu darasin da na fi sha’awa kamar tarihi da adabi. Don haka, ni mutum ce mai matukar sha’awar karatu sosai da kuma kallon fina-finai musamman da daddare, sannan idan na tashi da safe na shirya na tafi makaranta. Haka nan a ajin ma karatu nake ci gaba da yi, baya ga matukar sha’awar fina-finai da nake yi a lokaci guda.
Bugu da kari, ina matukar son ilimi yadda ya kamata, domin kuwa ban taba tunanin wata rana zan yi kokarin samar wa ko ba da izinin yin fim ba, amma sai wannan ya kasance kamar matsayin mabudin idanu a gare ni, sakamakon burin da nake da shi na fitarwa da kuma samar da fina-finai masu daman gaske. A duk lokacin da na kammala kallon wani fim, na kan tsaya na saurari abubuwan da suka wakana a bayan fage, na saurari hirarrakin da aka yi da daraktoci, masu tacewa da ‘yan wasa da kuma sauran jarumai, har na fahimta na kuma yi nazarin abubuwan da suka zo wa mutane a cikin fim din, ba ya ga wadanda aka dauka. Sannan nakan nutsu na saurari hirarrakin da aka yi da jaruman shirin, na saurari tarihinsu gaba daya, tattaunawa da irin yadda ‘yan wasan kwaikwayon ke kawo abubuwan da suka faru da kuma tasu fahimtar.
Sau tari na kan dauka cewa, duk abin da ake yi cikin shirin don ni ake yi. Shi yasa hakan ya kara min kwarin guiwar fito da sha’awata da kuma burina, domin gaskiya ni mai sha’awar kallon fina-finai ce sosai. Wannan tasa na kan fada wa kaina cewa, bari na gwada sa’ata na gani. Sannan akwai batun fito da mahaifina don a san wane ne shi da kuma irin gudunmawar da ya bayar wajen kyautata Arewaci da zaman lafiyar kasa baki-daya.
Baya ga wannan shiri na fito da tarihi (documentary) wane shiri kuma kike da shi a nan gaba?
Abin da ya sa na fara da wannan tarihi (documentary), saboda na fahimci sannu a hankali tarihi na zama abin sha’awa a wannan lokaci. Ina cikin dandamali da dama da suke haska tarihi daban daban masu yawan gaske, kamar na labarin rayuwa wanda ya faru a zahirance da irin na labarun ta’addanci, wannan dalili ne ya sa na ce bari na fara hada wannan tarihin (documentary). Baya ga haka ina matukar sha’awar shirya fim wanda zan rubuta labarin da kaina, na bayar da umarni, sannan na kuma fitar da shi ga jama’a. Har wa yau, na fahimci akwai karancin daraktoci mata a harkar fina-finai da masu shirya shi a masana’antar shirya fina-finai da a Nijeriya, an bar maza kadai sun mamaye bangarorin, duk da dai ba abu ne mai sauki a shiga masana’antar a canza wannnan ba, amma zan yi iyakar kokarina wajen kawo sauyi.
Har ila yau, ina samun kwarin guiwa tare da sha’awar irin ayyuka ‘yan kalilan na mata daraktoci, sakamakon yawan kallon ayyukansu. Kasancewar mata a matsayin daraktocin fina-finai, kan iya sauya Masana’antar. Dalili kuwa mata na da tunani iri daban-daban da zai iya ba su damar fitarwa da labarai fiye da yadda maza ke fitarwa. Na taba jin Sharon Stone ta ce, fina-finan da ta taka rawa a cikin su wanda maza suke rubutawa, ba sa iya fahimtar mata sosai, wanda hakan gaskiya ne.
Haka nan, kwata-kwata maza ba su fahimci inda mu mata muka dosa ba, don haka idan har mu da kanmu za mu rubuta fim mu bayar da shi ta yadda ya dace, shakka babu za a samu sauyi gagarumi, domin mun fi kowa sanin kanmu.
Me za ki iya tunawa a yarintarki musamman lokacin da kike tasowa a masarauta?
Babban abin da zan iya cewa a nan shi ne, Arewa da Masarautunsu na iya tsayawa kan ra’ayinsu, musamman ta fuskar bin tafarkin magabata a bangaren sarauta. Sannan ba su cika son bin duniya ta wasu hanyoyi ba, suna matukar son ganin sun rike sirri a dukkanin al’amuransu da al’adunsu. Ma’ana, suna da ra’ayi irin na ‘yan mazan jiya. Wannan ya sa yake da matukar wahala wajen fito da wani sabon abu sabanin wanda ke kunshe cikin al’adunmu na Arewa, shi ya sa masarautun suka shahara ake kuma tafiyar da su a haka.
Me ya sa Masarautunku na Gargajiya suka sha banban da sauran masarautun da kika sani?
Dalilin bai wuce idan aka yi la’akari da tarihi da kuma al’ada ba, bayan wannan, babu wani abu da zan iya karawa da shi. Sannan wajibi ne a matsayinmu na musulmai mu zama masu bin dokoki tare da sauran ka’idojin musulunci. Idan kuma muka kauce wa wannan tsari, za mu zama tamkar wadanda suka kauce wa hanyar bin daidai.
Don haka, dole ne mutum ya kula da matsayin jinsi; kamar yadda Allah SWT ya gindaya wa al’umma sharudda wajibi ne su bi, sannan dattawa na taka tasu rawar wajen yanke hukunci tare da kula a kan mene ne daidai, mene ne ba daidai ba. Amma ni a kashin kaina, ina yawan fitowa na yi magana kan abubuwan da nake kallo, wanda hakan a wasu lokutan na sani shiga damuwa.
Wace irin damuwa, ba mu misalan abubuwan da ke sa ki damuwa?
Wasu lokutan a cikin al’umma; musamman a lokacin da nake tasowa, a matsayina na yarinya a makaranta, wani lokacin mutum zai fito ya yi magana, amma abin da za ka ji na gaba shi ne wannan abin mamaki ne da ba a saba da shi ba. Yayin da ke kuma za ki yi tunanin fadin abin da kika fada a matsayin haka ne ya dace ki fada. A ce a matsayinki na yarinya musulma bai kamata ki a ce idan kika sanya kaya yadda kike son sanyawa a kalubalance ki ba, idan kika sa kaya ba ki sanya hijabi ba wasu za su kalle ki a matsayin wacce ba musulma tagari ko ta kwarai ba, ko kuma wacce ba cikakkiyar musulma ba.
Sannan ko ki sanya hijabi ko mayafi ko gyale da sauran su, rashin hakan sai a yi miki ca a kanki. Ni sam ban yarda da wannan ba; don haka ni ina da ra’ayin kamata ya yi mata musulmai su rika nuna zabinsu na sanya hijabi ko rashinsa; za su fi gamsuwa da jin dadi idan aka bar su da zabinsu.
A zahiri, don mace ba ta sanya hijabi ba, ba shi ne yake nuni da cewa ba ta yin sallah ko babu addini a tattare da ita ba. Lamari ne kawai na ra’ayin abin da mutum ke so na sanya hijabi ko kin sanyawa. ‘Yan mata musulmai da dama sun zabi ka da su sanya hijabi kwata-kwata ma a kowane lokaci, hakan shi ne yake nuni da cewa mu musulmai ne na banza ko ba musulmai na kwarai ba. Na san zai zama abun kunya ga fadin hakan, amma ni ina kokarin zama ta daban ce, domin ni musulma ce wacce na yi imani da ginshikai guda biyar na musulunci, sunana ma Zainab, sannan na kuma yi imani da ‘yancin bayyana ra’ayi, ‘yancin bayyana albarkacin baki da barin mutum ya rayu ta hanyoyin cimma burin mafarkansa.
Yanzu takamaimai me kike son cimma a wannan shiri naki na na tarihin Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero?
Abu mafi muhimmanci shi ne domin na bayar da tarihi da kuma labarin mahaifina. Cike nake da sanin cewa yaran wannan zamani, ba su da cikakken masaniya a kan shugabanninsu da kuma tarihinsu na baya. Wannan dalili ne ya sa na yi wannan tunani, saboda da zarar yau an ce babu tarihi, ba za mu taba ci gaba ba. Don haka, wajibi ne mu san abubuwan da suka wakana a baya. Saboda haka, ta sanin tarihi ne kadai za mu iya cimma irin wadannan abubuwa a wannan kasa. Koda a ce Ado Bayero ba mahaifina ba ne, ko shakka babu zan yi masa wannan sakamakon shekaru 51 da ya shafe yana masarauta, inda hakan ya ba shi dama sosai wajen shiga cikin kundin tarihin Nijeriya a bangarori daban-daban da kuma yin tasiri a gare su.
A bisa tarihi, an haifi mahaifina a zamanin mulkin mallaka, sannan ya zama sarki ne gaf bayan mulkin mallakar, ma’ana bayan samun ‘yancin kai. Ya kuma samu gogewa a bangaren siyasar Nijeriya daban-daban. Don haka, wannan tarihi (documentary) ya fito da dukkanin wadannan bayanai. Sannan kamar ni, hakan zai bai wa matasa da masu tasowa damar sanin tarihin Arewa da kuma mutumin da ya yi sarauta ya wakilci halifancin Fulani; wacce a kashin kanta tarihi ne mai matukar fa’ida da ta fara samun asali tun daga Uthman Dan Fodio a karni na 18. Kuma, daftarin tarihin zai taimaka wajen ilmantar da wayar da kai tare da nishadantar da jama’a dangane da tarihi da kuma al’adu. Amma kuma, akwai wani dumbin tarihin a Masarautar Kano wacce aka gina fadar tun a karni na 14.
Kasancewar ki daga Masarautar Arewa da ke da dinbin tarihi da al’ada, a ina kika samo salon wata rayuwa daban da wadda aka saba tun fil-azal?
Arewa kacokan na tafiyar da al’amuranta ne bisa al’ada da koyi da rayuwar ‘yan baya. Amma ni mahaifiyata ta tashi ne daga wani yanki na daban, ma’ana ba ‘yar Arewa ba ce. Ta fito ne daga Jihar Edo, amma dai musulma ce. Bugu da kari, mu mun taso ne a Kasar Ingila, wannan ne ya ba ni damar samun ‘yanci na yi rayuwata yadda nake so.
Amma idan aka yi la’akari da sauran ‘yan’uwana, ba su samu haka ba sakamakon ni mahaifiyata ba mutuniyar Arewa ba ce. Don haka, ni mahaifiyata ta raine ni ne da cikakken ‘yanci domin ita mace ce mai kwarin gwiwa. Sannan takan dauke ni mu yi tafiye-tafiye zuwa wurare daban-daban; ba mu cika zama a yankin Arewacin Nijeriya a kowane lokaci ba. Ta sa ni na samu ilmin zamantakewa a sauran yankunan Nijeriya kamar kudanci; kusan kowane lokaci galibi muna zama a Edo da kuma Jihar Legas.
Mafiya yawancin matan Arewacin Nijeriya ba su samu irin horon da za su samu kwarin guiwar yin wasu abubuwa kamar yadda na taso a ciki ba, sannan kuma irin wannan rayuwar da na samu kadan ne daga cikin mata musulmai ‘yan Arewa da suka samu irin ta.
Wane irin kwarin guiwa da goyon baya kika samu daga wajen ‘yan’uwanki, Masarauta da kuma Gwamnatin Kano kan wannan babban aiki naki?
Tun lokacin da na fito da wannan tunani da ra’ayi nawa, na fara ne a kashin kaina, sannan mahaifiyata ce mutum ta farko da ta mara min baya take taimako na. A lokacin da muke magana da ita kan shirina na hada wannan tarihi na mahaifina, sai ta ce da ni, “Eh, za ki iya yi. Domin kuwa, mahaifinki nagartaccen mutum ne; kuma hakan zai zama abu mai kyau.” Don haka, na yanke shawara na tsunduma cikin wannan aiki a kashin kaina, sannan maganar gudunmawa kuma babu wanda ya ba ni ko sisin kwabo. Iyalan mahaifina kuma dama su ne majinginata wadanda nake yin alfahari da su a kowane lokaci.
Duba da yadda sarkin ya kwashe shekaru sama da 50 a kan mulki, mene ne babban sirrin da ya sa ya rike masarauta har na tsawon wadannan shekaru?
Babu shakka ya yi mulki na tsawon rabin karni, sannan kuma shi ne sarki na biyu mai karancin shekaru a tarihin Kano. Domin kuwa ya haye karagar mulki yana da shekaru 33 a duniya, ya kuma rasu yana da shekara 83 da haihuwa, ‘yan watanni ne suka rage ya cika shekaru 84 Allah ya karbi kayansa. A nawa ganin, wannan shi ne dalilin da ya sa ya jima a kan karagar mulki a matsayin sarki. Kazalika, ya karbi mulki a hannun kawunsa, Mohammed Inuwa wanda ya rasu a lokacin, duk da dai shi watanni shida kadai ya yi a kan mulkin. Sannan akwai wasu muhimman abubuwa da dama a kasancewar sa na sarki.
Haka zalika, mutum ne mai kaunar zaman lafiya da kuma kokarin ganin ya faranta wa mutane da dama, musamman a lokutan da suke cikin damuwa, misali a lokutan zanga-zanga a Kano, ya kasance mai fadakar da jama’a muhimmancin zaman lafiya, kwanciyar hankali da ba da shawarwarin yadda za a shawo kan lamura a kuma zauna cikin koshin lafiya.
Wadanne kalubale kika fuskanta yayin hada wannan tarihi naki, sannan kuma wadanne matsaloli kika ci karo da su a kokarin hada shirin fim?
A zahirin gaskiya kowane abu mai muhimmin kan zo da nasa kalubalen da sauran matsaloli, kasancewar wannan shi ne karo na farko da na shirya da ba da umarni. A lokacin da na shiga hadawa gadan-gadan, ban ma tsaya tunanin kalubale da rashin fahimta ba, ban tsaya na daina tunanin ta yaya zan cimma nasara ba. Na tsunduma ne kawai tare da ci gaba da yin aikina. Kodayake, a gaskiya akwai wuya kam, amma na kasance mai jajircewa da jurewa har zuwa lokacin da na kai ga cimma gaci.
Bugu da kari, cike nake da farin ciki na ganin cewa na hada wani abu wanda jama’a za su kalla su kuma gani su saurara, musamman kalamai da na rubuta da ke magana kan rayuwar mahaifina, abun mamaki ne kwarai da gaske daga gare ni.
Ta yaya kika rubuta labarin shirin fim, kika ba da umarni kika kuma fita a ciki?
A’a, ba fa haka hakikanin abin yake ba. Na dai yi rubutu sosai, amma ban kai ga wallafawa ba, na rubuta wasu labarai da dama, wannan shi ne lokaci mafi kyau da kuma tarihi a gare ni.