Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
Abubuwan da za ku tanada:
Man Hulba, Zuma, Sassaken kuka, Cukwi, Aya, Bawon kankana
Yadda za’a hada:
Asamu man Hulba sai a gauraya shi da zuma mai kyau a dinga shan chokali biyu minti 30 kafin a ci abinci. Safe da rana da dare. Za’a sha na tsawon sati 3.
2- A samu sassaken babbar bishiyar kuka a daka a shanya ya bushe a sake dakawa ya zama gari, sai a samu Aya a soya ta sama-sama a daka ta zama gari, sai a samu bawon kankana a busar da shi a daka ya zama gari, sai a samu cukwi a daka ya zama gari.
Wadannan garin sai a hada su guri daya (awon su ya zama daidai) sai a kwaba da zuma a dinga shan cokali 2 bayan an ci abinci. Safe da rana da dare.
Sannan za’a iya gauraya wannan hadin garin da ruwan kankana a sa madara a dinga sha. Za’asha na tsawon sati uku.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp