Hanya ta 4: Lemon tsami: Asid din da ke cikin lemon tsami yana taimakawa wajen warkar da ciwo, kurajen fuska da kuma nankarwa.
Yanda ke amfani da shi:
- Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna
- Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi
A yanka Lemon tsami gida 2 sai a shafa shi a gurin da nankarwar take. A bar shi na tsahon mintuna goma sai a wanke da ruwan dumi. Ko kuma a hada ruwan Lemon tsamin da ruwan kukumba a shafa a wajen. A yi hakan a kullum idan ana san samun sakamako mai kyau.
Hanya ta 5: Man zaitun
Man zaitun yana dauke da sinadaran bitamin A da E wanda suke kara gudun jini zuwa karkashin fata da kuma kara laushin jiki. Suna kuma hana lalacewar fata.
Yanda ake amfani da shi:
A dan dumama man zaitun a wuta, kar ya yi zafi da yawa yanda zai kona fata. Sai a shafa a gurin da nankarwar ta ke. A yi hakan da safe da yamma a kullum.














