Gwamnan Jihar Ondo, Hon. Lucky Aiyedatiwa, ya samu tarɓa daga ɗumbin magoya baya a dandalin Dimokuraɗiyya (Democracy Park) da ke Akure ranar Juma’a bayan kotun ƙoli ta tabbatar da nasararsa. Gwamnan ya dawo ne daga Abuja inda aka yanke hukuncin da ya tabbatar da sahihancin zaɓensa.
A yayin jawabi ga dubban jama’a, Aiyedatiwa ya gode wa Allah, da mutanen Jihar Ondo da duk masu goyon bayansa a lokacin shari’ar. Ya bayyana kotu a matsayin ginshiƙin dimokuraɗiyya, yana mai jaddada cewa adalci da gaskiya suna da matuƙar muhimmanci wajen ɗorewar mulki. Ya kuma yaba wa lauyoyinsa kan ƙwarewarsu tare da gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa jagorancinsa.
- Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo
- Ƴansanda Sun Bankaɗo Maɓoyar Masu Garkuwa Da Mutane A Ondo
“Wannan nasara ba tawa ce kaɗai ba, ta kowa ce a Jihar Ondo,” in ji shi, yana mai ba da tabbacin kyakkyawan shugabanci da isar da alfanun dimokuraɗiyya ga jama’a.
A jawabansu na taya murna, wasu daga cikin manyan baƙi sun bayyana hukuncin kotun a matsayin nasarar jama’a. Hon. Ifedayo Abegunde na hukumar NDDC ya ce hukuncin ya tabbatar da cewa “ƙuri’un jama’a ba a ɓata su ba.” Tsohon mataimakin gwamna, Alhaji Abdulazeez Oluboyo, ya ce Aiyedatiwa ya kafa tarihi da samun nasara a ƙananan hukumomi baki ɗaya, yayin da tsohuwar kwamishina, Mrs. Omowumi Ohwovoriole, ta bayyana hukuncin kotun a matsayin ƙarshen duk wata muhawara kan zaɓen 2024.
Taron ya samu halartar jiga-jigan gwamnati da jam’iyya ciki har da Mataimakin Gwamna, Dr. Olayide Adelami; da Uwargidan Gwamna, Mrs. da Oluwaseun Aiyedatiwa; da Kakakin majalisar jihar, Rt. Hon. Olamide Oladiji; da Sakataren Gwamnati, Dr. Taiwo Fasoranti; da Shugaban Ma’aikata, Prince Segun Omojuwa; da mambobin majalisar zartarwa ta jiha; da manyan jiga-jigan APC; da shugabannin ƙananan hukumomi da na LCDA da sauran fitattun mutane.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp