Jordan Henderson ya ce zai buga wa Ingila wasa muddin zai iya duk da magoya bayan Ingilar suu yi masa ihu a wasan sada zumunci da suka doke Australia da ci 1-0 a Wembley ranar Juma’a.
Dan wasan tsakiyar mai shekaru 33, wanda ke taka leda a kulob din Al-Ettifaq na Saudiyya shine kyaftin din Ingila a wasan kuma an yi masa ihu lokacin da aka sauya shi bayan mintuna 62.
- Manchester United Zata Sayar Da Kashi 25 Na Kungiyar Akan Yuro Biliyan 1.3
- Nijeriya Da Saudiyya Sun Yi Kunnen Doki A Wasan Sada Zumunta
Ban ji dadin abin ba amma kuma hakan ba zai hana ni bugawa kasata kwallo ba muddin ta bukaci hakan in ji shi.
Henderson,wanda ya bugawa Ingila wasa sau 79, ya kara da cewa har yanzu ina son buga wa Ingila wasa muddin zan iya.
Henderson ya koma Al-Ettifaq a bazara a kan fam miliyan 12 daga Liverpool, inda ya kasance kyaftin.