Magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi sun yi zanga-zanga a Abuja, babban birnin tarayya kan zaben shugaban kasan da aka kammala a Nijeriya.
- An Gurfanar Da Mamu A Kotu Kan Zargin Daukar Nauyin Ta’addanci
- 2023: Jihohin Da INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamnoni
Masu zanga-zangar wadanda galibinsu matasa ne sun mamaye dandalin ‘Unity Fountain’ domin nuna bacin ransu.
Suna sanye da bakaken kaya dauke da alluna masu dauke da rubuce-rubuce daban-daban.
Da yake jawabi a wurin zanga-zangar, wanda ya shirya zanga-zangar, Moses Ogidi Paul, ya yi tir da gazawar INEC a zaben shugaban kasa da aka kammala.
Ogidi ya ce INEC ba ta makara wajen gyara kuskurenta ba.
Peter Obi dai ya kare a matsayi na uku a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 15 ga watan Fabrairu, yayin da Tinubu na jam’iyyar APC ya lashe zaben.