Musun kwallon kafa ya yi sanadin rasa ran wani magoyi bayan Manchester United a cibiyar kasuwanci ta Kyobgombe da ke yammacin kasar Uganda.
Benjamin Okello mai shekaru 22 ya rasa ransa sakamakon takaddama da wani mai goyon bayan Arsenal a ranar Lahadi, 27 ga watan Oktoba.
- Tawagar Likitocin Sin Ta Ba Da Gudummawar Kayayyakin Aikin Jinya Ga Asibitin Tanzaniya
- Sin Ta Zargi EU Da Bayar Da Kariyar Cinikayya Bayan Da Kungiyar Ta Kakaba Karin Haraji Kan Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin
Rikicin ya barke ne saboda murna bayan Arsenal ta tashi 2-2 da Liverpool a filin wasa na Emirates, kamar yadda jaridar Daily Monitor ta Uganda ta ruwaito.
Lamarin ya fara ne lokacin da Mohammed Salah ya zura kwallo a ragar Arsenal a filin wasa na Emirates, mai goyon bayan Manchester United Benjamin Okello ya tashi tsaye ya na murna, har cikin murna ya zubawa wani mai goyon bayan Arsenal gurguru a jiki yayin da yake murna.
Hakan ya kara ta’azzara lamarin, bayan an kammala wasan ne su biyun suka yi taho-mu-gama, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Benjamin Okello, bayan da wani mai goyon bayan Arsenal da ake kira Onan ya buge shi da sanda.
Shugaban karamar hukumar Kaharo, Mista Edmond Tumwesigye ne ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya bayyana samun labarin fadan da aka yi da safiyar Litinin.
Shaidu sun bayyana takaddamar ta fara ne a wani gidan kallo na yankin, inda magoya bayan Arsenal suka taru don kallon wasan.
Kwamandan ‘yansandan gundumar Kabale, Mista Joseph Bakaleke, ya bayyana cewa ‘yansanda sun samu rahoton faruwar lamarin.
Ya tabbatar da cewa daya daga cikin masu fadan daya ya mutu daga baya, wanda ake zargin Onan, wanda rahotanni sun bayyana cewa ya shahara da aikata miyagun laifuka a yankin.
Yanzu haka ‘yansanda na ci gaba da farautar sa.