• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mahaifina Ya Mika Kansa Ga ‘Yan Bindiga Suka Kashe Shi Don Ceton Rayuwarmu – Hajiya Asheku

bySulaiman
3 years ago
Bindiga

LABARAI MASU NASABA

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

Hajiya Asheku, ‘yar marigayi Alhaji Zakari Umaru Kigbu, ta bayyana yadda ‘yan bindiga suka halaka mahaifinta, tsohon kwamishinan hukumar kidaya (NPC) a gidansa da ke garin Lafiya cikin Jihar Nasarawa.

Asheku ta ce misalin karfe 11 na dare ne maharan suka shigo gidansu, amma suka gagara balle kofan shiga dakin mahaifinta, don haka sai suka fara neman yara a gidan, ganin haka sai Alhaji Zajari Umaru Kigbu ya fito daga dakinsa ya fuskanci ‘yan bindigan a lokacin da ya lura sun gano yaransa a ban-daki kuma suka ta kokarin harbin su domin ya ki fitowa.

  • ‘Yan bindiga Sun Kai Hari Kauyuka 8 Da Kashe 33 Da Sace Mutum 30 Da Shanu 2,000 A Kebbi Da Neja,

A ranar 28 ga watan Maris ne wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari gidan tsohon kwamishinan NPC, Zakari Umaru Kigbu, inda suka kashe shi, sannan suka sace dansa da kanwar matarsa. Kafin a kashe shi dai, Kigbu mai shekaru 60 da haihuwa kuma tsohon sojan saman mai ritaya yana koyarwa ne a kwalejin fasaha ta Isa Mustapha Agwai a Lafiya, (IMAP).

A yayin da ‘yan’uwa da abokan arziki ke ci gaba da jimamin rashin Alhaji Zakari Umar Kigbu, ‘yarsa mai shekara 29, Hajiya Asheku, cikin hawaye ta ba da labarin yadda makasan suka kashe mahaifinta ga ‘yan jarida.
Cikin kuka, Asheku ta ce, “Ni ce ta biyar cikin ‘ya’yan Zakari Umaru Kigbu kuma ‘yarsa mace tilo.
“A ranar da abin ya faru, ina zaune a falo a gidanmu da mahaifina da mahaifiyata da ‘yan’uwana muna kallon wani shiri a talabijin. Lokacin da muke kallon talabijin, mahaifina da mahaifiyata sun shiga dakinsu sun kwanta.
“Wasu cikin ‘yan’uwana suma sun ta fi sun kwanta, saboda abin ya faru ne misalin karfe 11 na dare.
“An bar ni a falo tare da dan’uwana wanda ke tura wasu abubuwa daga kwamfutarsa, kwatsam sai muka ji harbin bindiga. Daya cikin ‘yan’uwana ya yi maza ya rufe kofar kitchen da ta bulle tsakar gida.
“Wasu daga cikinmu mun ruga dakin mahaifinmu don mu boye, wasu kuma suka shiga dakin mahaifiyarmu.
“Yan bindigan, sun balle kofar gidanmu suka nufo dakin mahaifinmu. Da mahaifinmu ya lura dakinsa za su zo, sai ya umurci dukka mu mu fita mu ta fi store mu boye.
“Maharan sun yi kokarin balle kofar dakinsa, amma suka kasa saboda kofar na da karfi, sai suka fara neman mu.
“Da muka lura za su iya ganin mu cikin sauki a store, sai muka tafi ban-dakin mahaifyarmu muka boye, muna adduar Allah ya kawo mana dauki. Sun ta neman mu amma ba su gan mu ba.
“Suna cikin neman mu ne sai suka ji muna kus-kus a cikin ban-daki, nan take suka umurci mu fito ku su balle kofar su harbe mu dukkan mu. Saboda muna jin tsoro sai muka ki fitowa, sai suka umurci abokansu da ke waje su harbe mu ta tagar ban-daki. Sun fara harbe-harbe amma ba su same muba, domin duk mun kwanta.
“Ana hakan, mahaifinmu ya yi kokarin kiran ‘yan sanda da sojoji amma bai samu amsa mai gamsarwa ba. Don haka, ba shi da wata zabi sai ya fito daga dakinsa domin ya kare mu, a lokacin ne suka harbi mahaifina.
“Da muka ji karar harbin bindigan, dukkan mu mun fito waje muka gan shi kwance cikin jini.”
Asheku ta ce maharan su hudu ne kuma ba ta san ko harin na da alaka da siyasa ba.
Ta ce mahaifinta na harka da ‘yan siyasa, amma ba ta san dalilin da ya sa aka kawo masa harin ba
“Da suka zo, sun ce ba za su tafi ba sai sun kashe mahaifina a daren. Da suka harbe shi, dukkan mu mun fito mun gan shi cikin jinni, amma bai iya magana ba domin ya galabaita. Ya rasu bayan ‘yan mintuna.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Next Post
aure

Daga Zuwa Neman Aure: “An Kashe Min Da, ‘Yansanda Sun Mayar Da Ni Saniyar Tatsa”

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version