Allah ya yi rasuwa wa mahaifiyar fitaccen malamin addinin musulunci mazaunin jihar Kaduna, Sheikh (Dakta) Ahmad Abubakar Gumi.
A cewar malamin, jigo a ahlin Gumi ta rasu ne da yammacin ranar Lahadi a Kaduna.
Tunin aka yi mata jana’iza da kaita makwancinta a makabartar Unguwar Sarki da ke cikin garin Kaduna kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.
Sheikh Gumi, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, “Inna lillahi WA inna ilaihi rajiun. Yau da karfe 5:30 na yamma, cikin alhini da jimami, ina sanar da rasuwar mahaifiyata.
“Don Allah ku taya mu roka mata rahama da gafarar Allah.”
“Maganata da ita na karshe mako biyu da suka wuce. Ta ce min insha Allah, Allah zai sanyata da ‘ya’yanta da jikokinta a Aljannah.
“Wadannan kalmomin sun karfafeni sosai. Rahmatul lahi alaiha. Amin.”