A yau Laraba, aka sanar da rasuwar mahaifiyar tsohon jarumin Kannywood, Ahmed S Nuhu, wanda ya rasu shekaru 17 da suka wuce a ranar 1 ga Janairu, shekarar 2008.
Mahaifiyar S Nuhu ta rasu a birnin Jos, babban birnin jihar Filato, inda za a yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
- Sojin Ruwa Sun Yi Alƙawarin Ƙara Haƙo Gangar Mai Miliyan 3 A Kowace Rana
- Sojin Ruwa Sun Yi Alƙawarin Ƙara Haƙo Gangar Mai Miliyan 3 A Kowace Rana
Shugaban hukumar Fina-Finai ta Nijeriya, Ali Nuhu Muhammad, wanda kuma yana ɗaya daga cikin makusantan marigayin, ne ya sanar da rasuwar mahaifiyar tsohon jarumin a shafinsa na sada zumunta.