Allah ya yi wa Mahaifiyar tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Ghali Umar Na’abba, mai suna, Hajiya Rabi, rasuwa.
Wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP HAUSA cewa Hajiya Rabi ta rasu ne a Kano a daren Alhamis bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
- Allah Ya Yi Wa Babban Limamin Masallacin Garun Kura A Kano Rasuwa
- Allah Ya Yi Wa Mahaifiyar Mataimakin Abba Gida-Gida Rasuwa A Kano
Majiyar ta ce, za a yi sallar jana’izarta a ranar Juma’ar nan da misalin karfe 10:00 na safe a gidan Marigayi Alh. Bashir Tofa, da ke Unguwar Gandun Albasa, Kano.
Har ila yau, a cikin ‘Ya’yanta akwai Usaina Umar Na’abba, tsohuwar ma’aikaciyar gidan Rediyon Freedom da ke Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp