Allah ya yi wa, Hajiya Rabi Abdullahi, mahaifiyar dan takarar mataimakin Gwamnan Kano a karkashin jamiyyar NNPP, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo rasuwa.
Za a yi mata Jana’izarta a masallacin Alfurqan da ke Alu Avenue Nassarawa GRA da misalin karfe 4 na yamma.
Allah mata rahama, yasa Aljanna makoma, Amin.
Talla
Mun samu sanarwar rasuwar daga Sakataren Jam’iyyar NNPP na Kano, Dr. Hamisu Sadi Ali.
Talla