Mai magana da yawun majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) ya bayyana a yau Talata cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da ginshiki mai kwari da juriya mai karfi da mamammaki masu yawa da kuma kwazon gudanarwa mai fa’ida.
Mai magana da yawun taro na uku na majalisar karo na 14, Lou Qinjian ya shaida wa taron manema labarai hakan ne gabanin bude taron NPC da ke tafe.
- Za A Sake Gurfanar da Blatter Da Platini Kan Zargin Cin Hanci
- Majalisar CPPCC Za Ta Gudanar Da Taron Shekara-shekara Daga Ranar 4 Zuwa Ta 10 Ga Maris
Lou ya ce, a bara, kasar Sin ta cimma burinta na samun bunkasa da kimanin kashi 5 cikin dari, inda ya kara da cewa, kasar na da katafariyar kasuwa da cikakken tsarin masana’antu da ke tallafa wa ci gaban tattalin arzikinta.
Har ila yau, jami’in ya ce, adadin kudin da kasar Sin ta kashe a fannin tsaro idan aka auna da kason karfin tattalin arziki na GDP bai kai matsakaici na kasashen duniya ba.
Kazalika, ya ce, kasar Sin ta fara bayar da lamuni don maye gurbin basussukan kananan hukumomi da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 278.79 a bana. Kana ya kara da cewa, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin zai karfafa sa-ido kan yadda ake tafiyar da basussukan da gwamnati ke bi, musamman ma yadda ake maye gurbin boyayyen bashin da ake bin kananan hukumomi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp