A yau litinin mai shari’a Olukayode Ariwoola za a rantsar da shi a matsayin Alkalin Alkalan Nijeriya (CJN) bayan murabus din da Mai shari’a Tanko Muhammad ya yi daga mukaminsa na Alkalin Alkalai ba zato ba tsammani.
Mai magana da yawun Mai Shari’a Tanko, Ahuraka Isah, ya tabbatar da murabus din shugaban nasa ga LEADERSHIP a safiyar ranar Litinin.
Wata majiya sun shaida cewa za a rantsar da sabon Alkalin Alkalai (CJN) da karfe 11:00 na safiyar ranar Litinin.
In an rantsar da mai Shari’a Ariwoola, ana sa ran zai ajiye aikin alkalanci a shekarar 2028.
A halin da ake ciki dai, fadar shugaban kasa kawo yanzu ba ta ce uffan ba game da abubuwan da ke faruwa a bangaren shari’a a ‘yan kwanakin nan.
Cikakkun bayanai Daga baya…