Sassan duniya musamman manyan yankuna na ci gaba da kaka-ni-ka-yi da fargabar rashin tabbas saboda jirkitattun al’amuran da wasu masu kumbar susa ke kitsawa da nufin shamakance ci gaban wasu don kar a yi kafada da kafada da su.
A yayin da Turawan yamma ke ganin daukar matakin shamakancewa shi ne makamin ci gaba da babakerensu, musamman ta fuskar kimiyya da fasaha, ita kuwa kasar Sin na nuna cewa mai tsoron ta-mutu shi ke maho. Ma’ana, mai takure tunaninsa a wuri daya shi ne yake fargabar karewar wani abu ko kuma wani ya samu kwarewa irin tasa. Amma wanda zuciyarsa ke yalwace a kullum burinsa shi ne ba da dama ga wasu su samu ci gaba don ya san albarkar abun ba za ta kare ba.
- Akwai Bukatar Sin Da Masar Su Zurfafa Hadin Gwiwa Domin Kare Muradunsu
- Sin Ta Ware Yuan Biliyan 10 Don Shirye-Shiryen Ba Da Tallafin Aiki
Ba sai na tsaya lissafa hane-hanen sayar da fasahohin kayayyakin kimiyya da Amurka ke ta kakabawa ba, domin misalai nan birjik ko ina cikin kafofin sadarwa, kama daga batun fasahar abubuwan hada kayan laturoni na “semiconductors” zuwa su fasahar sadarwa ta kayayyakin kirkirarriyar basira, watau “chips” da sauransu.
A ganin kasar Sin, kimiyya da fasaha fage ne da ya kamata ya kawo hadin kai a duniya ba rarrabuwar kawuna ba. A bisa wannan fahimtar ta dukufa taka muhimmiyar rawa wajen karfafa musaya a tsakanin kasashen duniya da lalubo hanyoyin kara kawar da shingaye marasa ma’ana.
A wata tattaunawar da jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Sin a kwanan baya, Darakta-janar na shirin fasahar mahangar nesa na duniya (SKAO), Dr Philip Diamond ya jinjinawa yadda kawancen “ziri daya da hanya daya” (BRI) ke karfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin kimiyya da fasaha, inda ya ce, “hakika muna matukar martaba tsarin hadin gwiwar da ake karfafawa a karkashin BRI musamman bisa yadda ya fi mayar da hankali a bangaren gudanar da harkokin kimiyya masu bude kofa. Irin wannan hadin gwiwar yana karfafa imaninmu kan cewa ya kamata kowa da kowa ya ci gajiyar sha’anin kimiyya.”
Karuwar tasirin da kasar Sin ke yi a fagen ci gaban kimiyya da fasaha a duniya ba barazana ba ce, sai dai wata dama ce ta kawo ci gaba mai gamewa. Diamond ya kara da cewa, “Kasancewar na yi aiki kafada da kafada da wasu jami’o’i da cibiyoyin kasar Sin na tsawon shekaru masu yawa, na yi amanna da yadda kasar Sin ta dukufa ga samar da kimiyya da fasaha mai bude kofa ga duk duniya bisa adalci.”
Kazalika, masanin kimiyya, mamba a makarantar nazarin kimiyya da fasaha ta Afirka, Farfesa Felix Dapare Dakora, ya nuna yadda kasar Sin ke karfafa shigar kasashe masu tasowa cikin harkokin kimiyya a duniya. Yana mai cewa, “A halin yanzu, an gode da samuwar shirye-shiryen da kasar Sin ke mara musu baya a karkashin dandaloli kamar BRI, inda masana kimiyya daga kasashe masu tasowa ke samun damammakin da ba a taba ganin irinsu ba domin bayar da gudummawa da kuma zama a kan gaba.”
Jagorancin da kasar Sin ke yi wajen karfafa hadin gwiwa da kasashe masu tasowa ya bai wa kasashen damar fahimtar cewa lallai hadin kai shi ne karfin da ake bukata, kuma ana iya magance galibin matsalolin da suka zama karfen kafa sakamakon matakan masu shamakancewa, tare da tabbatar da cewa ba a bar kowace kasa a baya ba.
A kullum dai, mai burin ganin ci gaban wasu ba zai taba rasawa ba, kana mai tsoron ta-mutu kuma, zai ci gaba da yin maho! (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp