Majalisar Dokoki ta ƙasa (NASS) ta gabatar da sabon shirin da ke neman sauya jadawalin zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni na 2027 zuwa watan Nuwamba 2026, maimakon watan Fabrairu ko Maris kamar yadda aka saba.
Wannan mataki yana cikin gyaran dokar zaɓe ta 2022, wanda ya tanadi cewa zaɓe ya gudana kafin kwanaki 185 da ƙarewar wa’adin gwamnati mai ci, wanda ke ƙarewa a ranar 29 ga Mayu. Manufar shirin ita ce a samar da isasshen lokaci don kammala dukkan ƙorafe-ƙorafen dake gaban kotun zaɓe kafin rantsar da sabbin shugabanni.
- Ko Afirka Za Ta Samu Kujerar Dindindin A Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya?
- Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu
A yayin taron jin ra’ayoyi da kwamitin haɗin gwuiwa na majalisar dattijai da ta wakilai kan harkokin zaɓe suka gudanar a ranar Litinin, an bayyana cewa sabon tsarin zai taimaka wajen tabbatar da adalci da tsari a harkar zaɓe. Shugaban kwamitin majalisar wakilai, Hon. Adebayo Balogun, ya ce gyaran zai rage lokacin yanke hukunci na kotunan zaɓe daga kwanaki 180 zuwa 90, yayin da kotun ɗaukaka ƙara da kotun ƙoli za su yanke hukunci cikin kwanaki 60 da 35.
Ƙarin gyare-gyaren da aka gabatar sun haɗa da tanadin yin zaɓe da wuri ga wasu rukuni na mutane kamar jami’an tsaro, da ƴan jarida, da ma’aikatan hukumar zaɓe da masu sa ido na cikin gida, a ƙalla kwanaki 14 kafin babban zaɓe. Haka kuma, an ƙarfafa amfani da tsarin aika sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki domin tabbatar da gaskiya da inganci, tare da tanadin hukunci ga duk jami’in zaɓe da ya saɓa ƙa’ida ko ya yi sakaci wajen gudanar da aikinsa.
Wakilan hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC), ciki har da Farfesa Abdullahi Zuru, sun nuna goyon bayansu ga wannan shirin, suna mai jaddada cewa sauye-sauyen za su inganta tsarin zaɓe, da rage zargin maguɗi, da tabbatar da amincewar ƴan Nijeriya ga sakamakon zaɓe.
A cewar su, wannan sabon tsarin zai taimaka wajen gina dimokuraɗiyya mai ƙarfi da ɗorewa a ƙasar.