Sakamakon hauhawar farashin kayan abinci, majalisar dokokin Jihar Sakkwato ta bukaci gwamnatin Jihar da ta dakatar da fitar da kayan abinci zuwa wajen jihar.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudurin da Honarabul Shamsu Aliyu (APC- Wurno) ya gabatar a zaman majalisar a ranar Alhamis 15 ga watan Fabrairun 2024.
- Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnoni Kan Ƙalubalen Da Nijeriya Ke Fuskanta
- Hukumar Zaɓe Ta Jihar Katsina Ta Ayyana Ranar Gudanar Da Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Jihar
Wannan na daya daga cikin matakan shawo kan halin kunci da jama’a ke ciki na hauhawar farashi wanda ya shafi al’ummar jihar da kasa bakidaya.
Dan majalisar ya bayyana cewa, wajibi ne gwamnati ta dauki kwararan matakai musamman duba ga rahoton da Bankin Duniya ya fitar kwanan nan kan sha’anin samar da abinci.
Ya ce, rahoton ya yi hasashen jihohi bakwai da za su iya fuskantar matsalar karancin abinci daga watan Mayu kuma jihar Sakkwato na daya daga ciki.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Honarabul Bashar Isa Jabo dan majalisar da ke wakiltar Tambuwal ta Gabas a jam’iyyar PDP ya bayyana muhimmancin ganin gwamnati ta bayar da kulawa ta musamman wajen inganta jin dadin al’umma.
Dan majalisar ya bayyana aikin kawata birnin jihar da gwamnati ke yi a matsayin wanda baida matukar muhimmanci musamman bisa la’akari da halin kunci da jama’a suke ciki.
Majalisar dokokin dai ta aminta da bukatar bayan da shugaban majalisar, Honarabul Tukur Bala ya bukaci jin ra’ayin masu shata dokoki wadanda suka kada kuri’ar amincewa baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp