Majalisar Dattijai ta kuduri aniyar bayar da goyon bayanta ga Babban Bankin Nijeriya (CBN) don sake fasalin takardun kudi na N1,000, N500 da N200.
Majalisar ta yi wannan kudiri ne bayan tafka muhawara kan kudirin da Sanata Uba Sani ya gabatar kan manufar CBN na sake fasalin kudin Nairar guda uku.
- Sin Za Ta Kara Raya Sana’o’in Dake Shafar Kasuwar Sinadarin Carbon
- Takarar Musulmai 2: Asiwaju Ya Gana Da Shugabannin CAN, “Kiristoci ‘Ya’yana Ne” —Tinubu
Yawancin Sanatoci a sassan jam’iyyu na goyon bayan sake fasalin kudin amma wasunsu na nuna damuwa kan wa’adin da babban bankin ya sanya na ajiye tsofaffin takardun kudi a bankunan kasuwanci.
‘Yan majalisar sun kuma nuna shakku kan tasirin sake fasalin kudin Naira ga tattalin arzikin kasar nan da kuma idan hakan zai taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma raguwar darajar Naira.
Sun bukaci Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya yi karin haske kan wadannan batutuwa.
Sun kuma damu da tasirin wannan manufa ga wadanda ke yankunan karkara da wadanda ba sa hulda da banki.
Don haka majalisar ta umarci kwamitinta kan harkokin banki da ya fara sa ido sosai don tabbatar da cewa an kare ‘yan Nijeriya yayin wannan aiki.
Emefiele a ranar 26 ga Oktoba, 2022 ya sanar da cewa babban bankin zai fitar da sabbin takardun kudi na N200, N500, da N1,000, daga ranar 15 ga Disamba, 2022, yayin da sabbin kudaden da ake da su da kuma na yanzu za su ci gaba da tafiya tare har zuwa 31 ga Janairu, 2023.