Me ake nufi da Salatin Istika? Sallar Istika tana daya daga cikin addu’o’in Sunnah da Annabi Muhammad (SAW) yake yi a lokacin fari, ko yunwa ko lokacin zafi mai tsanani.
Sallar ta kunshi raka’a biyu kuma ana fara takbirai bakwai a raka’ar farko, sannan takbirai shida a raka’a ta biyu.
Limamin yakan karanta suratul a’ala da suratul ghasiya a kowace raka’a. bayan idar da sallah limamin sai ya yi huduba daga karshe ya yi addu’a kamar yadda sunnah ta tabbatar da haka.
Talla