Majalisar Wakilai ta karyata zargin yunkurin tsige kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila.
A wani karamin zaman da ‘yan majalisar suka yi, sun karyata cewar wasu jiga-jigan majalisar da suka fito daga arewacin Nijeriya na kitsa tsige Femi kan maganar turka-turkar gabatar kudurin samar da ruwan sha.
- Gwamnatin Kaduna Ta Ba Da Hutun Kwana 3 Don Jama’a Su Yi Rijistar Katin Zabe
- Goje Ya Raba Taki Na Naira Miliyan 300 Ga Manoman Gombe
A cewar ‘yan majalisar, abin takaici ne wallafa wannan rahoton, inda suka nanata cewa, daukacin ‘yan majalisar na goyon bayan Femi.
Daga baya, an tura maganar ga kwamitin ladaftarwa na majalisar don a gudanar da cikakken bincike.
Kudurin wanda zai kasance a karkashin kulawar Gwamnatin Tarayya, an gabatar da shi ne tun farko a zamanin majalisar na takwas, amma ‘yan majalisar suka ki amince wa da shi.
Sai dai, an sake gabatar da kudurin a zamanin majalisar ta tara, amma kudurin, ya ci karo daga gun wasu ‘yan Nijeriya da kuma ‘yan majalisar wadanda suka yi tunanin cewa kudurin zai janyo raba kan kasa.
An kuma sake gabatar da kudurin a zaman majalisar a ranar 29 ga watan Yuni 2022.
Dan majalisar Sada Soli, wanda ya dauki nauyin kudurin ya sanar da cewa, an yi tuntuba a kan kudurin, inda ya yi nuni da cewa, in har kudurin zai janyo matsala zai janye shi daga gaban majalisar.