Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta umarci hukumar Shari’ah da ta gaggauta gudanar da bincike kan bidiyon da ke yawo a kafafen sadarwa zumunta inda aka jiyo wani malamin addinin Muslunci da ke Kano, Dakta Abdallah Gadon-Kaya na zargin cewa, akwai wasu da suka taru a jihar Bauchi su na luwaɗi da maɗigo gami da auren jinsi.
Ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Chinade/Madara, Dakta Nasiru Ahmed Ala, shi ne ya gabatar da ƙudurin neman a gayyato malamin bisa buƙatar gaggawa lura da muhimmanci hakan a yayin zaman majalisar na ranar Talata.
- An Kaddamar Da Shirin “Afirka a Cikin Fina-Finai” Zagaye Na Biyu
- Dangote Ya Ceto Nijeriya Daga Durƙushewa – Otedola
Ala, ya bayyana cewa, Malamin addinin, Sheikh Gadon-Kaya, ya shaida wa duniya cewa, masu luwaɗi da maɗigo daga sassan jihohin arewacin Nijeriya, sun haɗu a Bauchi domin sheƙe ayarsu har ma da auren jinsi lamarin da ya ce ya saɓa wa koyarwar addinin musulunci da na Kiristanci.
A cewar ɗan majalisar, akwai buƙatar hukumar Shari’a ta jihar ta gayyaci Dakta Abdallah Gadon Kaya domin ya zo ya bada hujjojin iƙirarin nasa domin tabbatar da dokokin Shari’a su yi aiki a kan duk wanda aka samu da laifi.
A nasa ɓangaren, Kakakin majalisar dokokin jihar, Abubakar Y. Sulaiman, ya ce, kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, ya bai wa majalisar ƙarfin ikon gayyatar kai tsaye ga wani mutum da ya bayyana a gabanta domin gudanar da wani bincike ko neman ƙarin haske kan kowani bayani da ya shafi ƙasa ko kuma iƙirarin da ya yi.
Idan za a tuna dai tun da farko, hukumar Shari’a ta aike da katin gayyata ga Dakta Abdallah Gadon-Kaya domin ya zo ya mata ƙarin haske da cikakken bayani kan iƙirarin nasa da ke zargin wasu da haɗuwa a Bauchi domin yin luwaɗi da maɗigo, amma tun daga wannan lokacin ba a sake jin komai daga wajen hukumar ba.
A wani matakin na daban, ƙudurin dokar kafa hukumar HISBA ta jihar Bauchi na 2024 ya tsallake karatu na biyu a gaban majalisar.