Shugaban kamfanin samar da wutar lantarki na Geregu, Femi Otedola, ya bayyana cewar matatar Dangote ta kawo karshen rara-gefe da Nijeriya ke yi wa manyan kasashen duniya domin wadata kasar da makamashi.
Attajirin, ya ce matatar da Dangote ya gina ta samarwa Nijeriya ‘yancin da ta ke bukata daga dogaro ga kasashen duniya.
- Ministan Ma’adanai Ya Bukaci Masu Harkar Ma’adanai A Jihar Nasarawa Su Zauna Lafiya
- Kasashen Yamma Na Yunkurin Cimma Burinsu Ta Hanyar Goyon Bayan Philiphines
Otedola, ya ce gina matata mai tace ganga dubu 650 kowace rana ba karamin aiki ba ne.
Ya yaba wa Aliko Dangote wajen shawo kan duk matsalolin da ya fuskanta lokacin aikin, tare da yaba wa shugab Bola Tinubu saboda goyon bayan da ya ba shi.
Otedola, ya yi waiwaye kan yarjejeniyar da suka kulla da Dangote shekara 25 da suka gabata na kafa kamfanin Blue Star domin sayen hannayen jarin matatar Fatakwal da na Kaduna, inda Aliko zai mallaki kashi 51, shi kuma ya mallaki kashi 20 kafin gwamnatin wancan lokacin ta soke shirin.
Otedola, ya ce Dangote a yanzu ya hambarar da attajiran da suka mamaye bangaren man suka kuma hana Nijeriya sukuni wajen kaddamar da gagarumar matatarsa.