Majalisar Wakilai ta yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta ganin sun ceto sauran dalibai mata 30 na Jami’ar Tarayya ta Gusau ta Jihar Zamfara da ke hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
Hakan ya biyo bayan amincewa da wani kudiri na majalisar mai muhimmanci ga al’umma, wanda Hon. Kabiru Ahmadu daga jihar Zamfara a ranar Talata ya kawo.
- Za Mu Dasa Wa ‘Yan Nijeriya Dabi’ar Gaskata Kalaman Shugabanni A Zukatansu – Minista
- Kotu Ta Daure Dillalin Tabar Wiwi Shekara 10 A Kano
Hon. Ahmadu da ya jagoranci muhawarar, ya nuna damuwarsa kan makomar sauran ‘yan matan da ke hannun wadannan ‘yan fashin dajin.
Ya kuma koka da yadda wadannan ‘yan fashin dajin ke ci gaba da addabar al’umma a yankin Arewa maso Yamma.
Dan majalisar ya yi kira ga babban hafsan tsaron kasa da babban sufeton ‘yan sanda da su gaggauta ganin an sako ‘yan matan daga hannun ‘yan fashin dajin.
Hon. Inuwa Garba a tasa gudunmuwar ya bayyana cewa, lamarin yana da tada hankali ganin yadda makarantun ilimi ke zama cikin tsoro saboda babu tsaro a makarantun ganin yadda ‘yan fashin suka mayar da Makarantu wurin ta’addancinsu musamman a yankin Arewacin Nijeriya.