Majalisar Wakilai ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya kawo sabuwar dabarar kawo karshen kashe-kashe, sace-sace da sauran ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Zamfara da ma kasa baki daya.
Wannan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na kula da muradun jama’a da dan majalisa mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta jihar Zamfara, Hon. Kabiru Amadu, ya gabatar a zaman majalisar a ranar Talata.
- Gwamnonin Arewa Sun Nemi A Gaggauta Ceto Ƴan Makaranta Mata Ta Kebbi Da Aka Yi Garkuwa Da Su
- PDP Ta Yi Allah-wadai Da Sace Ɗalibai Mata A Kebbi
A yayin gabatar da kudirin, Amadu ya bayyana cewa, idan aka yi la’akari da kalubalen tsaron da “yaki ci yaki cinyewa” a Jihar Zamfara da ma fadin kasar, za a iya cewa, “gwamnati ba ta yi abin da ya dace ba don kare rayuka da kadarorin ‘yan Nijeriya don ba su damar gudanar da ayyukansu na yau da kullum.”
Ya bayyana cewa, ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a sassan Zamfara inda suka kashe mutane sama da 10, suka sace mutane 130 sannan suka sanya haraji mai yawa har Naira miliyan 100 ga wadannan al’ummomi masu rauni.
Amadu ya ce, ‘yan bindigar suna gudanar da ayyukansu na ta’addanci a kan babura dauke da akalla mutane biyu zuwa uku a kan kowane babur, suna sintiri daga wannan al’umma zuwa wancan na tsawon makonni biyu zuwa uku dauke da makamai ba tare da wata barazana daga hukumomin tsaro ba.














