Majalisar Dattawa ta amince da tsohon hafsan sojin ƙasa, Janar Christopher Musa (mai ritaya), a matsayin sabon Ministan Tsaro bayan tantance shi da ta ɗauki kusan awanni biyar.
A lokacin tantancewar, Musa ya ce zai inganta tsaro ta hanyar haɗa kai tsakanin sojoji, ’yansanda, sauran hukumomin tsaro da al’ummomi.
- Kasar Sin Ta Zama Babbar Kasuwar Da Fim Din “Zootopia 2” Ya Samu Kudi
- Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ya Sauka Beijing Domin Ziyarar Aiki
Ya yi gargaɗin cewa ’yan ta’adda na kai hare-hare a Nijeriya ne saboda suna ganin ƙasar tana da arziƙi.
Ya kuma yi alƙawarin magance giɓin tsaro da kuma ƙara haɗin gwiwa da ƙasashen maƙwabta.
Ya yi nuni da cewa sojoji kaɗai ba za su magance matsalar tsaro ba, ya jaddada buƙatar kyakkyawar gwamnati da goyon bayan al’umma.
Sanatoci sun yaba da ƙwarewarsa kuma suka amince da shi baki ɗaya.
Musa zai jagoranci harkokin tsaro a Nijeriya yayin da ake ci gaba da fama da hare-haren ta’addanci, satar mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga.














